✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

dangwari da ’yan sanda

Wani Bagwari ne ya je kasuwa yana aikin dako, sai rigima ta kaure; ’yan sandan kwantar da tarzoma suka zo kasuwar suna tambayar mutane daya…

Wani Bagwari ne ya je kasuwa yana aikin dako, sai rigima ta kaure; ’yan sandan kwantar da tarzoma suka zo kasuwar suna tambayar mutane daya bayan daya. Suna cewa: “Kai wane ne, mene ne aikinka.” Kowa yana amsa tambayoyin daidai yadda ake bukata. Sai tambaya ta zo kan dangwari, aka tambaye shi mece ce sana’arsa. Maimakon ya amsa da cewa yana sana’ar dako ne, sai ya ce: “Mu muna daukar kayan mutane ne.” Nan take ’yan sandan suka kama shi, suka saka shi motarsu.
Daga Isah Gazzali Idris Bichi, Mazaunin Wuse-Abuja 07052228805