✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

dangote zai kafa tashar wutar lantarki

Shugaban Rukunin Kamfanonin dangote Alhaji Aliko dangote zai kafa tashar samar da  hasken wutar lantarki mai karfin Megawatt 500 domin inganta samar da hasken wutar…

Shugaban Rukunin Kamfanonin dangote Alhaji Aliko dangote zai kafa tashar samar da  hasken wutar lantarki mai karfin Megawatt 500 domin inganta samar da hasken wutar lantarki a jihohin Kano da Jigawa da Katsina da kuma Kaduna ta yadda za a farfado da kamfanoni da masana’antu a wadannan jihohi hudu.
Wannan albishir ya fito ne daga Daraktan Rukunin Kamfanonin, Injiniya Mansur Ahmed a wani jawabi da ya yi wajen bikin baje koli a Kano, inda ya sanar da cewa dangote yana sha’awar ganin cewa masana’antu da kamfanoni da ke wannan sashe suna farfadowa ta yadda tattalin arziki zai kara inganta.
Har ila yau, ya bayyana cewa idan aka kammala aikin ginin tashar wutar lantarkin, harkokin kasuwanci za su kara habaka, sannan za a samu karin hanyoyi na dogaro da kai kamar yadda ake gani a sauran kasashen duniya wadanda  suka bunkasa ta fuskar masana’antu.
A karshe Injiniya Mansur ya ce Alhaji Aliko dangote ya yi nisa wajen tallafa wa al’umma ta fannoni masu tarin yawa da suka hada da kula da lafiya da ilimi da sauransu.