Hamshakin Attajirin nan dan asalin Jihar Kano, Alhaji Aliko Dangote, ya zamo mutum na 117 cikin jerin mutane 500 mafiya arziki a duniya.
Wannan na kunshe cikin sabbin alkaluman da Jaridar Bloomberg, mai yawaita kididdiga kan mutane mafiya arziki a duniya ta fitar.
Jaridar ta kan fitar da bayananta ne bayan lissafi da tattara dukiyar da kowane attajiri ya mallaka wanda take kira Bloomberg Billionaire Index.
Alkaluman da Jaridar ta wallafa sun nuna cewa a yanzu Dangote ya mallakin dukiyar da ta kai Dala biliyan 17.8 ($17.8bn).
Mutumin da ya kasance na daya a duniya a yawan dukiya shi ne Elon Musk wanda ya mallaki $194bn. Sai Jeff Bezos da ya yi kankan da Musk a mataki na biyu da $194bn.
Gabanin wannan lokaci, Bezos, tsohon shugaban Kamfanin Amazon wanda a baya nan ya dawo daga duniyar wata, ya yi wa duk wani attajiri zarra a doron kasa.
Mutuwar aurensa da matarsa, MacKenzie Scott na daya daga cikin sabubabban da suka janyo arzikinsa ya ragu, inda a yanzu take mataki na 22 a jerin mafiya arziki a duniya bayan ta mallaki dukiyar da kai $59bn.
Attajiri na uku a duniya shi ne Bernard Arnault wanda ya mallaki $174bn.
Kafin wannan lokaci, mai kamfanin Microsoft Bill Gates ke rike da matsayin inda arzikinsa ya ragu bayan rabuwa da matarsa, Melinda French Gates a kwanakin baya.
Mai shafin Facebook Mark Zuckerberg ke mataki na biyar inda ya mallaki dukiyar da ta kai $135bn.
Larry Page na mataki na shida wanda ya mallaki dukiyar da ta kai $123bn yayin da Sergey Brin ya biyo bayansa a mataki na bakwai da $118bn.
Warren Buffet da ya mallaki $104bn shi ne cikon na takwas sai Steve Balmer da dukiyar da ta kai $103bn a mataki na tara da kuma Larry Ellison da ya mallaki $103bn a mataki na goma cikin jerin mutane 500 da Jaridar ta fitar.