Matatar mai ta Dangote ta rage farashin man fatur zuwa Naira 899.50k kan kowace lita a safiyar ranar Alhamis.
Kamfanin ya ce an ɗauki matakin rage farashin ne don samar da sauƙi da ’yan Nijeriya ke buƙata lokacin hutun ƙarshen shekara.
- Ana fargabar mutuwar yara da yawa a turmutsitsi a Ibadan
- Manufofina sun fara farfaɗo da tattalin arziƙin Najeriya — Tinubu
“Matatar mai ta farko mai zaman kanta a Afirka, wacce a baya ta rage farashin man zuwa N970 kan kowace lita a ranar 24 ga Nuwamba, yanzu kuma ta sanar da sabon farashin zuwa N899.50 kan kowace lita.
“An tsara wannan ragin ne don sauƙaƙe farashin sufuri a lokacin bukukuwan shekara,” a cewar sanarwar da Babban Jami’in Sadarwa, Anthony Chiejina ya sanya wa hannu.
Ya ƙara da cewa kamfanin ya kuma gabatar da wani tayi na musamman domin ƙara amfanar abokan hulɗar su.
“Duk da haka kan rangwamen hutun, matatar man Dangote na bai wa masu amfani da damar sayen ƙarin litar man fetur a kan bashi ga kowace lita da aka siya akan tsarin biyan kuɗi.”
“Don rage farashin sufuri a wannan lokacin hutu, matatar Dangote tana ba da rangwamen hutu a kan man fetur. Daga yau man fetur ɗin mu zai kasance akan Naira 899.50 akan kowace lita a wajen dakon manyan motocinmu. Haka kuma, duk litar da aka saya a kan tsabar kuɗi, masu amfani za su sami damar siyan litar a kan bashi, tare da amincewar banki daga bankunan Access, bankin First Bank, ko bankin Zenith Bank,” in ji Chiejina.