Hamshakin attajirin nan na Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya dada lulawa sama a jerin attajiran duniya.
A yanzu dai yawan abin da ya mallaka ya kai Dalar Amurka biliyan 17.8, sabanin a bara da yake da Dala 14.8.
- WAEC ta sanar da ranar fara jarrabawar WASSCE ta 2021
- ‘An tafka ruwan da ba a taba yin irinsa ba a Katsina cikin shekara 100’
Hakan dai ya sa ya kasance dan Najeriya daya tilo da ya shiga jerin manyan attajiran duniya da Bloomberg take fitarwa a kowacce shekara.
Kimanin attajirai 120 ne suka shiga jerin sunayen da Bloomberg din ta fitar ranar Litinin.
Sauran ’yan nahiyar Afrikan da suka shiga jerin sun hada da Johann Rupert da iyalansa wadanda sula mallaki $10.1bn; Nicky Oppenheimer wanda ya mallaki $7.80bn da kuma Natie Kirsh mai $7.15bn, dukkansu daga Afirka ta Kudu.
Nassef Sawiris na kasar Masar kuma yana biye musu baya da $6.93bn.
Shekaru takwas kenan a jere Dangote yana jan zarensa a matsayin attajirin Afirka ba kakkautawa.
Har yanzu dai Ellon Musk da Jeff Bezos sune ke kan gaba a matsayin wadanda suka fi kowa kudi a duniya inda suka mallaki Dala biliyan 194 kowannensu, yayin da Bernard Arnault ke biye musu baya da $174bn, sai kuma Bill Gates wanda ya mallaki $148bn.
Mark Zuckerberg, mamallaki shafukan sada zumunta na Facebook da Intagram da WhatsApp shi yake biye musu baya a matsayi na biyar da $135bn.
Aliko Dangote dai shi ne shugaban rukunin kamfanonin Dangote, kuma shi ne yake da kamfanin siminti mafi girma a nahiyar Afirka.
Kazalika, attajirin yana harkar sukari da gishiri da takin zamani da kuma wasu kayan abinci.
Ko a kwanakin baya sai da wata mujallar kasuwanci da tattalin arziki ta duniya da ke kasar Burtaniya mai suna Richtopia ta ayyana shi a matsayin mutum na takwas mafi taimako a duniya.
Hakan na zuwa ne bayan ya kara yawan abin da yake warewa gidauniyarsa ta Aliko Dangote Foundation (ADF) zuwa kusan $1.25bn.