Kungiyar jama’atul izalatil bidi’a wa’ikamatussuna a jihar Gombe, ta yi Allah wadai da wasu mutane da suka danganta Ministan sadarwa na kasa Dokta Isa Ali Pantami, da ayyukan ta’addanci.
Shugaban kungiyar a jihar, Injiniya Salisu Muhammad Gombe ne ya bayyana hakan a lokacin wani taron manema labarai, inda ya ce tun kuruciyar Isa Ali bai da abokin fada domin ya tashi ne yana harkar neman ilimi.
- Shin dagaske an haramta yin tashe a Kano?
- George Floyd: Kotu ta tabbatar da laifin kisan bakar fata da aka yi a Amurka
Salisu Gombe, ya ce wasu marasa kishin kasa da ke fada da musulunci da basa kaunar ci gaba da irin abubuwan alheri da Ministan yake yi ne suke alakanta shi da ta’addanci.
Ya ce, kasancewarsa Malamin addini mai kamanta gaskiya ne ya sa wata Jami’a a Madina ta dauke shi karantarwa.
Sannan kuma ya ce hazakar Pantami ce ta sanya Shugaba Muhammad Buhari ya nada shi Shugaban Hukumar Bunkasa Fasahar Zamani (NITDA), wanda sai a lokacinsa ne wasu ’yan Arewa suka san da hukumar kuma daga bisani ya sake nada shi Minista a wa’adinsa na biyu.
A cewar Malamin, marasa kishin kai ne da suke ganin an hana su yin warwason dukiyar kasa ke jifan Ministan da kalaman batanci wanda kuma ko shakka babu yin hakan zalunci ne.
Ya ce sun gode wa Allah wadanda suka fara fitowa suna yi masa yarfe, sun janye kalamansu don haka sauran ma da suke da irin wanna akida su gaggauta janyewa.
Kazalila, Injiniya Gombe ya ce Sheikh Pantami tun baya cikin gwamnati yake yaki da tsattsauran ra’ayi “domin shi ne ya fara zaunar da Muhammad Yusuf, shugaban Boko Haram na farko, ya gaya masa wanna akidar da suke yi ba addini bace.”
“To ya za’a yi wanda ya fito ya kalubalanci ’yan ta’adda za’a ce masa dan ta’adda,” a cewar Injiya Gombe.
A karshe, ya yi kira ga Sheikh Pantami, da cewa kar ya biye wa masu kushe ya yi kasa a guiwa kan rin ayyukan ci gaba da yake kawo wa kasar.