✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

#Dancingforhusband: Yadda gasar rawa ga miji ke ta da kura

Wani sabon salo da ke tashe a kafafen sadarwa na zamani a ’yan kwanakin nan, inda ake nuna ma’aurata, a lokuta da dama mata, suna…

Wani sabon salo da ke tashe a kafafen sadarwa na zamani a ’yan kwanakin nan, inda ake nuna ma’aurata, a lokuta da dama mata, suna rawa yayin kai wa mazajensu abinci, wasu kuma mazan suna rawa suna yi wa matan likin kudi, ya bar baya da kura.

Shi dai wannan sabon salon ana kiransa #dancingforhusbandchallenge, wato gasar yi wa miji rawa.

Aminiya ta gano hotunan bidiyo da dama suna yawo a kafafen sadarwa, inda suke tayar da kura da jawo cece-kuce.

Wasu da dama suna yabon abin a matsayin soyayya, wasu suna ganin kawai shashanci ne da rashin kishi.

A hotunan bidiyon da suke yawo, ana sanya wakar fitaccen mawaki Hamisu Breaker mai suna Jaruma.

Wani ‘ya saki matarsa’

A wani rahoto da ba a tabbatar ba, an samu labarin cewa wani ya saki matarsa saboda ta saki hoton bidiyon rawar da suka yi.

Da yake bayyana sakin a shafinsa na Facebook, wani fitaccen marubuci a shafukan sadarwa na zamani, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya ce, “Innalillahi wa inna ilaihirrajiun. Yanzu nake samun labarin cewa wani tsohon maigidana ya saki matarsa saboda ta saki faifan bidiyon rawarsu na #Dancingforhusband a daren jiya.

“Babban abin bakin cikin ma shi ne shekararsu 19 da aure, da yara 3. Ita kadai ce matarsa. Allah Ya kyauta.”

Da yake tsokaci a kan wannan sako na Sanusi Bature, fitaccen dan jarida Jafar Jafar ya ce, “Duk da ba na goyon bayan wannan sabon salon shashancin, amma in dai wannan ne dalilin to bai kyauta ba.”

Shi ma matashin dan siyasar nan kuma dan jarida, Adnan Mukhtar Tudunwada, cewa ya yi a matsayin martani ga tsokacin Jafar Jafar, “Gaskiya dai, maigida! Mene ne na saki a kan wannan?”

Ka’idar gasar

Bincike ya nuna cewa Aisha Falke ce ta shirya gasar (Hoto: Legit)

Bincike dai ya nuna cewa mai shafin “Northern Hibiscus” a Instagram Aisha Falke ce ta assasa gasar, bayan ta ci karo da bidiyon wata da ta yi wa mijinta rawa yayin da wakar ta Hamisu Breaker ke tashi.

Daga nan ta sa kyautar wasu kudi cewa duk wacce ta fi burgewa za a ba ta, sannan ta shata ka’idojin shiga.

Ka’idojin dai su ne mace ta sanya riga bubu ta leshi, hannunta fal da awarwaron gwal, a samu falo mai kyau, miji ya zauna a kujera, sannan a sanya wakar Hamisu Breaker ta Jaruma.

Aminiya ta tuntubi Aysha Falke don jin ta-bakinta game da gasar, amma ta ki cewa komai.

“Idan kun shirya ku kira ni sai mu yi magana a hukumance”, inji ta, sannan ta kashe wayarta.

Ra’ayin ’yan Kannywood

Saratu Gidado, wato Daso, ta rika sanya bidiyoyin a shafinta na Instagram, inda a kasan daya daga cikinsu ta wallafa cewa, “Sallar bana dai ana soyewa a sohiyal midiya. Kun yarda ni ma in turo nawa bidiyon?”

Sai Abba el-Mustapha ya mayar da martani da cewa, “Idan ba ta yi ba yanzu a yi wuf da shi.” Hakan na nuna amincewarsa da bidiyon.

Ita kuma Mansurah Isa cewa ta yi, “Mama ai sai na zo mu yi wallah. Gobe mu hadu.”

Shi ma Baballe Hayatu ya ce, “soyayya a Tokyo.”

A daya daga cikin hotunan bidiyon, Mansurah Isa cewa ta yi, “wannan mutumin ya saba zuwa biki. Yadda yake lika kudin, za ka gane.”

A wani bidiyon ma, Sayyada Sadiya Haruna cewa ta yi, “Corona sannu da aiki.”

A wani bidiyon, Baballe Hayatu ya ce, “Mai gidana ashe ka iya rawa kaima? Ma sha Allah. Bana dai matan Hausawa sai su janye cewa mazan Hausawa ba su iya soyayya ba.”

Abin da mutane ke cewa

Wani mai suna Aminu Abdullahi Mai Unguwa cewa ya yi, “Allah Ka sa matar da zan aura ta min haka har karshen rayuwarmu.”

Ita kuma wata mai suna Hauwa’u Bujawa cewa ta yi, “Ji shi don Allah kamar gunki. Ya ki ya nuna ma ya ji dadin, to ai shi ke nan.”

Wani mai suna Safiyanu kuma cewa ya yi, “Ni fa har yanzu ban ga kin gwado gidan talakawa ba. Kawai gidajen masu hannu da shuni ne.”

Ita ma wata mai suna Fatima Zahra cewa ta yi, “Oh ni! Dole su tashi ai sun ga yara suna ta yin wuf da mazan nasu.”

Saif Zango cewa ya yi, “Muna godiya wannan ai shi ne gyara aurenki kada a sha ki basilla, ehe.”

Shi kuma wani mai suna Danmaje cewa ya yi, “Allah mun tuba kada yara su gani.”

Shi ma Anbo Abba cewa ya yi, “Wannan auren ba daraja.”

Shi ma Umar Ibn Muhammad cewa ya yi, “Wannan soyayya ko fitsara.”

Umar Galadima ya ce, “wannan kuma wani sabon is… ne ya taso matan aure su rika daukar bidiyo da mazansu na sunna suna turawa a duniya kowa na gani? Uhmmm! Allah Ya kyauta.”

Aminiya ta tuntubi mai shafin na ‘Northern Hibiscus’ domin taa bakinta a kan wannan lamari, inda ta ki cewa komai.

Wasu daga cikin hotunan da muka tsakura daga bidiyoyin