✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan wasan Pillars Odoji ya rasu a hadin mota

A ranar Lahadin da ta gabata ce dan wasan tsakiya na kungiyar Kano Pillars, Chinedu Odoji ya rasu sakamakon hadarin mota. Chinedu Odoji wanda tsohon…

A ranar Lahadin da ta gabata ce dan wasan tsakiya na kungiyar Kano Pillars, Chinedu Odoji ya rasu sakamakon hadarin mota.

Chinedu Odoji wanda tsohon dan wasan Eyimba ne da ya dawo Pillars a kakar wasa ta bana ya rasu ne a hadarin da ya auku  da misalin karfe 2:30 na rana lokacin da yake tuka mota a kan titin Independence a Unguwar Bompai da ke Kano.

A takardar da Kano Pillars ta fitar dauke da sa hannun Kakakinta Rilwanu Idris Malikawa ta bayyana kaduwa kan rasuwar dan wasan inda ta bayyana  dan wasan a matsayin mai sadaukar da kai. 

Malikawa ya ce bayan hadarin an kai gawar marigayin Asibitin Murtala, kuma “Yanzu haka shugabannnin kungiyar suna bin hanyoyin da suka kamata domin mika gawar ga iyalansa don binnewa,” inji shi.

Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana rasuwar Odoji da bababn rashi da jihar ba za ta taba mantawa da shi ba, inda ya yi alkawarin taimaka wa iyalan marigayin a wannan lokaci da suke ciki na radadin rashin marigayin. 

Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano Alhaji Ibahim Galadima ya bayyana rasuwar Odoji da babban rashi ga Pillars da Najeriya baki daya.