✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan wasan kwaikwaiyo, Kasagi Na Halima ya rasu

Marubucin littafin Kulba Na Barna ya rasu bayan fama da rashin lafiya.

Allah Ya yi wa fitaccen marubuci kuma dan wasan kwaikwayo na dauri, Umaru Danjuma Katsina, wanda aka fi sani da Kasagi na Halima, rasuwa.

Kasagi wanda shi ne marubucin littafin Kulba Na Barna, ya rasu ne da asubahin ranar Juma’a 29 ga watan Oktoban 2021.

Dokta Bashir Abu Sabe ya tabbatar wa Aminiya cewa Allah Ya yi wa fitaccen dan wasan kwaikwayon kuma marubucin rasuwa ne a wani asibiti a Katsina, bayan gajeruwar jinya.