Shugaban Kwamitin Rikon Kwarya na Kasa na Jam’iyyar PDP, Sanata Ahmed Muhammed Makarfi ya bayyyan yadda jam’iyyar za ta gudanar da batun karba-karba a zaben da za a yi a shekarar 2019.
Ya ce shugabannin jam’iyyar za su tabbatar cewa ra’ayin ’yan jam’iyyar ne zai yanke hukunci daga karshe.
Makarfi ya yi furucin ne a tattaunawar da ya yi da manema labarai a gidansa da ke Kaduna inda ya ce PDP za ta bi salon da ta bi a zaben fidda gwani na shugaban kasa da ta yi a baya inda wadanda ba su amince da karba-karba ba za su yi takara amma daga karshe jam’iyyar ce za ta yanke hukunci.
Kwamitin da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu, ya jagoranta shekarar da ta gabata ya bayar da shawarar cewa dan takarar mukamin shugaban kasa zai fito daga Arewa sannan kuma shugaban jam’iyyar na kasa zai fito daga Kudu, matakin da jam’iyyar ta amince da shi a babban taron jam’iyyar na kasa da ya gudana a garin Fatakwal.
Makarfi ya bayyana cewa tsarin bai canja ba kuma jam’iyyar na bukatar ’ya’yanta su amince da tsarin.
“Wannan shi ne matsayin jam’iyyar. Duk abin da ya shafi jam’iyyar to daga shugabannin jam’iyyar za a ji shi ba daga wani mutum ba, shi ya sa nake cewa batun karba-karba bai canja ba. Hukunci ne na jam’iyyar wanda aka yanke shi tun a babban taron jam’iyyar a garin Fatakwal a watan Mayu kuma hukuncin da aka yanke a babban taron jam’iyyar shi ne hukuncin karshe”. Inji shi.
Gwamna Ayo Fayose na Jihar Ekiti ya bayyana cewa zai tsaya takarar neman mukamin shugaban kasa a jam’iyyar a shekarar 2019.