✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan takarar Gwamnan Kano a LP ya gana da Tinubu

Ganawar ta gudana ne a yayin da ake tsaka da rade-radin dan takarar zai yi fatali da aniyar tasa.

Dan takarar Gwamnan Jihar Kano na Jam’iyyar LP, Bashir I. Bashir, ya gana da dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC mai mulki, Bola Tinubu.

Ganawar ta gudana ne a yammacin Lahadi a Abuja, yayin da ake tsaka da rade-radin dan takarar zai yi fatali da aniyar tasa.

Hotunan ganawar tasu a Abuja sun nuna wasu kusoshin jam’iyyar a tare da Bashir da Tinubu.

Sai dai har yanzu dan takarar bai sanar da ajiye takarar tasa ba, ko kuma komawa APC a hukumance.

Kodayake ba a bayyana makasudin tattaunawar ba, amma tana zuwa ne kasa da mako biyu bayan Bashir ya kaurace wa yakin neman zaben dan takarar jam’iyyarsu na shugaban kasa, Peter Obi a Jihar Kano.

Sai dai duk kokarinmu na jin ta bakin dan takarar kan batun ya ci tura, saboda bai amsa kira ko rubutaccen sakon da wakilinmu ya aike masa ba, har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Bashir dai, wanda daya ne daga cikin manyan ’yan takarar Gwamnan Kano a zabe mai zuwa, na cikin mutum ukun da suka halarci taron muhawarar da rukunin kamfanonin Media Trust ya shirya a Kano a makon da ya gabata.