Wani dan bindiga da ya karya yarjejeniyar sulhu a Karamar Hukumar Jibiya ta Jihar Katsina mai suna Bala Wuta na Garin Mazanya, na can kwance rai-kwakwai-mutu-kwakwai bayan ya sha dukan kawo wuka.
Tubabbun ’yan bindiga sun yi wa Bala wuta takakkiya ne har gida inda suka yi masa bugun dawa, bayan da ya yi garkuwa da wasu matafiya jim kadan bayan sulhun da aka yi, inda bayan sun lugwiwita shi, suka wajabta masa biyan tarar Naira miliyan uku.
- HOTUNA: Fashewar tankar gas ta kashe gomman mutane a Legas
- HOTUNA: An hana Gwamna Fubara shiga Majalisar Dokokin Ribas
Ana iya tuna cewa, a ranar 28 ga watan Fabrairu, 2025 ne aka yi sulhun, wanda ya samu wakilcin sojoji da ’yan sanda da sauran jami’an tsaro da masu ruwa karkashin jagorancin shugaban karamar hukumar ta Jibiya Alhaji Maitan, kamar yadda su ’yan bindigar suka nema.
’Yan bindigar da suka halarci zaman a karkashin jagoransu Audu Lankai, sun hada da Kantoma da Ori da Tukur Dan Najeriya da Bammi da sauransu da suka fito daga yankin Zamfara.
Yarjejeniyar da aka kulla
Jama’ar yankin sun shimfida wa ’yan bindiga sharadin barin kai hare-hare a fadin karamar hukumar da hanyar Katsina zuwa Jibiya da hanyar Jibiya zuwa Gurbi da kuma wadda ke zuwa Batsari.
Za kuma su da daina kai hari ko barna a gonaki ko cikin daji ko guje-guje a kan babura a cikin garin ko nuna rashin da’a ko tarbiyya ga al’umma.
Kazalika, yarjejeniyar ta bukaci za su kiyaye duk dokokin gwamnati su kuma daina yawo da makamai a bainar jama’a.
A nasu bangaren, tubabbun ’yan bindigar dajin sun shardanta a daina kashe su ko kama dabbobinsu babu dalili da kuma tabbatar da adalci a tsakaninsu da sauran al’umma a matsayinsu na ’yan kasa.
Sa’annan sun bukaci a daina daukar doka da hannu a rika barin hukuma ta yi hukunci ga mai laifi.
Bayan nan ne suka sako mutane 10 na garin Daddara da ke hannunsu tare da mika bindiga kirar AK-49 guda biyu.
Bala Wuta ya ji a jikinsa
Sai dai duk da wannan yarjejeniyar sulhu da aka kulla, sai ga shi a ranar Alhamis da ta gabata, wani wanda bai shiga sulhun ba mai suna Bala Wuta na Garin Mazanya da ya addabi hanyar zuwa Jibiya, ya kayar da wata mota ya yi awon gaba da matafiya a Mallamawar Batsari — garin su Lankai.
A dalilin haka shi Audu Lankai jagoran sasanci ya taras da shi har gida ya yi mishi dukan kawo wuka sannan ya sanya masa tarar kudi har naira milyan uku.
Har zuwa yanzu, wakilinmu ya ruwaito cewa, Bala Wuta yana can kwance yana jin jiki a garin na Mazanya.
Labarin da muka samu daga garin na Jibiya an ce, a ranar Lahadi an ga Fulanin da ke cikin dajin sun shigo kasuwa mazansu da matansu cikin murna saboda samun wannan ’yanci.
Majiyarmu ta shaida mana cewa, Fulanin sun rika sayen lemon kwalba mai sunyi da ake sayarwa Naira 250, wanda suke cewa a can daji naira dubu ake sayar musu.