Wani matashi mai shekara 32 da ake zargin yana ta’ammali da miyagun kwayoyi ya shake mahaifiyarsa har lahira a yankin Ijebu-Ode da ke Jihar Ogun.
Dan uwan wanda ake zargin ne ya gano cewa an kashe mahaifiyarsa bayan ya dawo daga aikin gadi da yake yi.
- Ban ci bashin N10bn na CCTV ba – Ganduje
- Abba El-Mustapha ya zama shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano
An kama matashin mai suna Samson ne lokacin da makwabta suka gano cewa yana da hannu a mutuwar mahaifiyarsa kuma daga bisani suka mika shi ga ‘yan sanda.
Wata majiya ta bayyana cewa wanda ake zargin ya kasance dan shaye-shaye, wanda ya bar gidansu tsawon shekara biyar sai daga bisani ya dawo.
Da ta ke tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin ‘yan sandan Ogun, Omotola Odutola, ya ce rundunar ta san da faruwar lamarin.
A cewar Odutola, wanda ake zargin a halin yanzu yana da tabin hankali.
Kakakin ta bayyana cewa a baya ’yan uwan Samson sun taba daure shi da igiya don hana shi yi wa kansa rauni.
“Ya kai wa mahaifiyarsa a lokacin bukukuwan Sallah, kuma rahotanni sun bayyana wna kula da lafiyarsa.
“Har yanzu ba a san ko wani abu ya faru tsakaninsa da mahaifiyarsa ba, amma bincike na farko ya nuna cewa tun a wannan rana, an daure shi a gidan, sai dai an gano ya shake mahaifiyarsa,” in ji ta.
Odutola ta ce an samu alamun tashin hankali a tsakaninsa da mahaifiyarsa.
“Samson Sikiru har yanzu yana hannun ‘yan sanda, amma ba a samu wani bayani daga gare shi ba,” in ji ta.