Tsohon Kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano, Mu’azu Magaji wanda aka fi sani da Dan Sarauniya, ya gaza cika sharudan beli da wata kotu a Jihar Kano ta gindaya masa.
A kan haka ne Dan Sarauniya wanda ya yi kaurin suna wajen sukar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a kafafen sada zumunta ya sake shigar da wani roko a gaban kotun yana neman ta yi masa sassauci kan sharuddan belin da ta gindaya masa.
- A dauki mataki kan mutanen da suka kawo gurbataccen man fetur —Buhari
- INEC ta kammala shirin zaben Kananan Hukumomin Abuja
A cewar wata majiya mai tushe daga Ma’aikatar Shari’a ta Kano wadda Jaridar Justice Watch News ta tattaro, ta ce Lauyan Dan Sarauniya, Barista Garzali Datti Ahmad ya shigar da rokon ne a ranar 9 ga watan Fabrairun 2022.
Bayanai sun ce sanarwar mai dauke da sa hannun Barista Garzali Datti Ahmad, tana rokon kotun ta sake duba sharuddan belin da ta sanya wa Dan Sarauniya a karon farko.
Ana iya tuna cewa, Alkalin kotun Majistare mai lamba 58 da ke zamanta a Nomanslan, Mai Shari’a Aminu Gabari ya amince da bayar da belin Mu’azu Magaji bisa sharuddan ajiye kudi Naira miliyan 1 da gabatar da mutane biyu wadanda za su tsaya masa.
Daga cikin wadanda Mai Shari’a Gabari ya nemi Dan Sarauniya ya gabatar sun hada da biyu daga cikin; dagacin unguwarsa, Kwamandan Hukumar Hisbah ko kuma Babban Limamin Karamar Hukumar Dawakin Tofa.
Kari a kan haka, Kotun ta kuma umurci Mu’azu Magaji da ya ajiye fasfo dinsa na tafiye-tafiye a wurin magatakardan kotun.
Wakiliyarmu ta ruwaito cewa, har yanzu dai wanda ake tuhumar yanzu bai iya cika sharuddan ba, domin kuwa Kwamandan Hisbah ko kuma Babban Limamin Dawakin Tofa da Dagacin unguwar da Dan Sarauniya ya fito babu wanda ya halarci kotun domin sanya hannu a kan takardar belin.
A makonnin da suka gabata ne aka gurfanar da Dan Sarauniya a gaban kuliya bisa zargin bata suna da cin mutuncin gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, zargin da ya musanta
Lauyan masu kara, Barista Wada A Wada, daya daga cikin manyan lauyoyi a Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano, ya shaida wa kotun cewa wanda ake kara ya aikata laifin ne tsakanin shekarar 2021 zuwa 2022 a shafinsa na Facebook.
Wada ya yi zargin cewa wanda ake tuhumar ya saka hoton Gwamnan Ganduje tare da wata mace da har yanzu ba a tantance ba a shafinsa na Facebook wanda yake ikirarin cewa gwamnan yana neman mata.
A cewarsa, laifin ya ci karo da sashe na 392 da 399 da 114 na kundin laifuffuka.
Sai dai kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 2 ga Maris, 2022 don ci gaba shari’ar.