✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan sandan da ya yi tatul da giya ya hallaka maigidansa

Ana zargin wani dan sanda mai mukamin Sajan da kashe maigidansa mai mukamin Sufeta bayan ya yi tatul da giya. Wasu ganau sun ce dan…

Ana zargin wani dan sanda mai mukamin Sajan da kashe maigidansa mai mukamin Sufeta bayan ya yi tatul da giya.

Wasu ganau sun ce dan sandan da ake zargin ya shawo giya ne a wata mashaya da ke kusa da gidan da yake haya a unguwar Oko-Oba a Legas a karshen makon jiya.

Shaidun sun ce bayan da ya dawo gida cikin daren sai ya hau makwabtansa da fada kamar yadda ya saba, inda ya dauki adda ya yi kan wani makwabcinsa da ita.

Ganin hakan ne ya sa abokin aikinsa mai mukamin Sufeta ya yi yunkurin ya shiga tsakani, amma sai Sajan din ya hau shi da sara lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar Sufetan.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Legas DSP Bala Elkana ya shaida wa Aminiya cewa Sajan din mai suna Okema Azuquo yana tsare a hannun rundunar.

“A cikin dare 4 ga watan Yuni ne wani mutum mai suna Azees Adebayo da ke zaune a unguwar Dosumu a yankin Agbelekale Oke-odo, ya shigar da kara a caji ofis cewa wanda ake zargin ya hau mutanen da suke haya da fada.

“Ya yiwa wani dan sanda mai mukamin Sufeta mummunan rauni da adda a lokacin da Sufetan mai suna Adekunle Ilesanmi wanda ke zaune a gida guda da wanda ake zargin ya yi kokarin shiga tsakanin wanda ake zargin da makwabcinsa a lokacin da ya hau makwabcin nasa da fada.

“Makwabcin mai suna Ayodele Eyitayo ya samu karamin rauni kuma an sallame shi daga asibiti, shi kuma Sufetan ya rasu bayan an kwantar da shi a asibiti sakamakon munanan raunuka da Sajen ya yi masa”, inji shi.

Bala Elkana ya ce rundunar ‘yan sanda ta aike da sakon ta’aziyya ga iyalin dan sandan da ya raau kana tana tsare da dan sandan da ake zargi wanda za a gurfanar a gaban kotu da zarar an kammala bincike.