Wata kotu mai hukunta laifuka na musamman da ke da zamanta a Ikeja a jihar Legas ta daure wani korarren jami’in dan sanda Ologunowo Ojo na shekara bakwai a kurkuku.
Kotun ta daure shi ne saboda laifin harbe wani mutum mai kimanin shekara 45 mai suna Taiye Akande da bindiga kirar AK47 kuskure.
Da take yanke hukuncin, Mai Shari’a Oluwatoyin Taiwo ta ce laifin nasa ya saba da Sashe na 224 na Kundin Manyan Laifuka na Jihar Legas na 2015.
Alkalin ta ce an samu rahotannin yadda ’yan sanda ke kashe mutane ba bisa ka’ida ba suna fakewa da cewa kuskure ne.
Ta ce tana sa ran hukuncin ya zama izina ga sauran jami’an tsaro a nan gaba.
“Ya aikata laifin ne cikin ganganci ba tare da girmama rayuwar dan Adam ba.
“Za a cire lokacin da ya shafe a tsare (shekara daya da wata uku) daga cikin wa’adin zamansa na gidan kaso”, inji alkalin.
Dan sanda mai shigar da kara, O.A Bajulaiye-Bishi ya shaida wa kotun cewa wanda aka yanke wa hukuncin ya aikata laifin ne da misalin 7:30 na daren uku ga Fabrairu, 2020, lokacin yake gadi a kamfanin Frajend Investment da ke Shapati Akodo, Ajah, Legas.
Ya ce, “An garzaya da Taiye zuwa asibitin Akodo kafin daga bisani ya mutu a can”.
To sai dai korarren dan sandan ya ce ba shi da niyyar kashe marigayin.