Sojoji sun kona ofishin ’yan sanda da ke yankin Ogijo a Jihar Ogun kan zargin kashe wani abokin aikinsu da wani dan sanda ya yi da wuka.
Bayanai sun ce sojoji sun kai harin tare da banka wa ofishin ’yan sandan wuta ne sanye da kaki ba tare da sunayensu a jikin kakin ba.
Rahotanni sun ce lamarin dai ya haifar da rudani a tsakanin jama’ar yankin na tsawon sama da sa’a guda da sojojin suka ci karensu babu babbaka.
Majiya daga ’yan sanda
Majiya daga ’yan sanda ta ce sojojin da lamarin ya shafa sun fito ne daga Bataliya ta 174 a yankin Ikorodu, Jihar Legas.
Ta kara da cewa sun kai samamen ne don daukar fansa kan abin da wani dan sanda ya aikata wa abokin aikinsu.
Ana zargin dan sandan da ne da daba wa sojan wuka a kirji saboda sa-in-sar da ta shiga tsakaninsu.
Lamarin da ya fusata abokan aikin marigayin, inda suka bi sawun dan sandan wanda ya tsere tare da neman mafaka a ofishin ’yan sanda na Ogijo.
Da yake tofa albarkacin bakinsa kan lamarin ta shafinsa na Twitter, jami’in hulda da jama’a na ’yan sandan Jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya ce, “Muna sanar da jama’a cewa lamarin ya faru ne a Ogijo, Jihar Ogun, wanda ke kusa da Ikorodu a Jihar Legas.”
Martanin Rundunar Soja
A nata martanin, Rundunar Sojojin Najeriya ta ce, “Fusatattun matasa da suka shaida abin da ya faru ne suka yi amfani da wannan dama wajen kai wa ofishin ’yan sandan hari.”
Hakan na kunshe ne cikin sanarwar da rundunar ta fitar a ranar Alhamis dauke da sa hannun Mataimakin Darakatan Hulda da Jama’a, na Runduna ta 81, Laftanar-Kanar Olabisi Ayeni.
Ya ce sojoji sun tsare wanda ake zargi don kare rayuwarsa tare da mika shi ga ’yan sanda domin bincike.
Bayan faruwar lamarin “An garzaya da sojan Asibitin Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Legas da ke Odogunyan inda aka tabbatar da mutuwarsa.
“Kuma an dauki gawar zuwa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Bataliya ta 174 da ke Ikorodu,” in ji jami’in.