Wani sufeton dan sanda ya bude wa abokan aikinsa wuta mai mukamin Kofur sannan ya raunata wani mataimakin sufeto, wato DSP.
A cewar rundunar ‘yan sandan Abuja ta ce daga bisani sufeton wanda bata bayyana sunansa ba ya harbe kansa har lahira a ofishin ‘yan sandan da ke unguwar Dutsen Alhaji a Karamar Hukumar Bwari a babban tarayya Abuja.
Kwamishinan rundunar ‘yan sandan Abuja Bala Ciroma, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:30 na asubahin jiya Lahadi, sannan ya umurci a gudanar da bincike domin gano musabbabin lamarin da kuma daukar matakan kare sake aukuwar hakan.