Wani dan sandan da ke gadin bankin First Bank na garin Saminaka da ke jihar Kaduna, ya harbe wani kurma mai suna Musa Munka’ilu har lahira.
Ana zargin dan sandan ya harbe wannan kurman ne a yayin da ya harba bindigarsa sama, lokacin da suke hayaniya da wani matashi da yazo bankin yana kokarin shiga ta karfi, duk da cewa an riga an tashi.
- NAJERIYA A YAU: Shin Karin Kudin Ruwa Zai Hana Tsadar Kayan Masarufi?
- Facebook ya kaddamar da manhajar gano yaran da suka bace a Najeriya
Wata majiya da abin ya faru a kan idonta, ta shaida wa Aminiya cewa matashin ya kafe kan cewa sai ya shiga cikin bankin.
Haka ta sanya hayaniya ta tashi, shi ne sai ’yan sanda da ke gadin bankin, suka fito daga ciki a fusace, suka bi wannan matashi, suna ture shi.
A dai dai lokacin ne sai daya daga cikin ’yan sandan ya harba bindigarsa, shi ne sai harsashinta ya je ya sami wannan kurma a lokacin da yake wucewa ta gaban bankin, nan take ya fadi kasa jini na zuba daga jikinsa, har rai ya yi halinsa.
Wannan abu da ya faru ya fusata matasa, inda suka yi ta jifan bankin da duwatsu kafin jami’an tsaro, su tarwatsa su.
Da yake zantawa da Aminiya, mai gidan wannan kurma, mai suna Alhaji Babangida Malami, ya ce sun yi shekara 37 suna tare da marigayin.
Ya yi kira ga hukuma da ta sa a biya diyya ga marayun da ya bari, domin ya rasu ya bar matarsa da yara kanana shida; mata hudu maza biyu, kuma babbar ’yarsa ta isa aure.
Shi ma da yake zantawa da Aminiya, kan lamarin, Shugaban Kungiyar Kurame ta Karamar Hukumar Lere, Danladi Dauda Unguwar Jumare, ya ce wannan bawan Allah, ya fito daga wajen taron da suke yi na kungiyarsu zai wuce ta gaban bankin harsashin ya same shi.
Aminiya ta tuntubi Kwamandan Rundunar ’Yan Sanda na shiyyar Saminaka, ACP Ibrahim Jibrin, kan wannan lamari.
Ya tabbatar wa Aminiya cewa za a tura wadanda ake zargi kan wannan zuwa hedkwatar rundunar da ke Kaduna, domin fadada bincike a kansu.