✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan sakandaren Najeriya ya damfari ’yar Kambodiya Naira miliyan 27

Yanzu haka ’yan sanda suna gudanar da bincike kan wani saurayi dan makarantar sakandare mai shekara 19 mai suna Chigemezu Arikibe da suke zargi da…

Yanzu haka ’yan sanda suna gudanar da bincike kan wani saurayi dan makarantar sakandare mai shekara 19 mai suna Chigemezu Arikibe da suke zargi da damfarar wata ’yar kasar Kambodiya Naira miliyan 27 ta hanyar Intanet.

Ana zargin saurayin da bayyana wa matar mai suna Sophanmia a shafukansa na Facebook da Instagram cewa shi Ba’amurke ne matukin jirgin sama da ke aiki da Kamfanin Jiragen Sama na Birtaniya, inda bayan ya tabbatar da alaka ta kullu a tsakaninsa da matar, sai ya yi mata tayin aike mata da wani sako mai muhimmanci da tsabar kudi Dalar Amurka dubu 500, domin ta zuba masa jari a harkar saye da sayar da gidaje a kasarsu ta Kambodiya.

Ana zargin matashin ya shaida wa Sophanmia cewa zai aike mata da sakon ne ta hannun wani kamfanin aikewa da sakonni da ke kasar Indonesiya, inda ya umarce ta ta aike wa kamfanin Dala 800 domin ta karbi sakon.

Bincike ya nuna cewa daga nan ne ya tuntubi wani abokin damfararsa da ke kasar Indonesiya, cewa ya yi magana da matar a matsayin shi ne mai kamfanin aikewa da sakonnin, kuma ya karbi kudin daga matar.

Binciken farko na ’yan sanda ya gano cewa bayan matar ta aike da kudin ne, sai Arikibe ya fara ba ta uzurorin da suka sa sakon bai iske ta ba, kuma ya ci gaba da matsin lamba a kan ta tura masa Dala dubu 75.

Sai dai dubunsa ta cika ne a lokacin da matar ta gano cewa, yaron da ke ikirarin cewa shi Ba’amurke ne matukin jirgin sama daga Najeriya yake ta kiranta ba Amurka ba. Sai ta sanar da Ofishin Jakadancin Nijeriya da ke Kambodiya, inda suka sanar da ’yan sandan Najeriya, inda ’yan sandan musamman a Ofishin Sufeto Janar, karkashin jagorancin DCP Abba Kyari suka shiga farautarsa.

Wata majiyar ’yan sanda ta ce, masu binciken sun gano wanda ake tuhumar a yankin Mbaitoli a Jihar Imo. “Mun kama wanda ake tuhumar tare da layi da wayar da ya saba kiran matar da shi, bayan da muka binciki wayar duk mun ga maganganun da ya rika yi da matar. Da muka bincike shi, ya amsa aikata laifin, sannan ya ce akwai wani abokin damfararsa da ke zaune a kasar Indonesiya wanda yake taimaka masa amso kudin daga asusun wani bankin kasar Amurka. Ya yi ikirarin cewa shi asalinsa Ba’amurke ne, hakan ne ya sanya ya bai wa matar lambar asusun bankin da ke Amurkar,” inji majiyar.

Ta kara da cewa: “Abu mafi muni shi ne matar ta ciwo bashin kudaden da ta tura masa ne  daga wani bankin kasarsu.”

Arikibe, ya ce ya koyi damfara ta Intanet ce daga wani abokinsa, inda a cikin mako daya ya fara aiwatar da nasa. Ya ce, “Na yi makarantar sakandare ta Community School a garin Eziooha a Karamar Hukumar Mbaitoli, na kammala a shekarar 2018. Abokina Ugochukwu ne ya koyar da ni yadda ake damfara ta Intanet. Na kuma bude shafina na karya a Fakebook da sunan Frank William, kuma a shafin Instagram na bude da Patrick William. “Duk kuma na cika su ne da hotunan wani matukin jiragen sama dan Amurka. Daga baya ne ainihin mai hotunan ya gano cewa ina amfani da hotunansa, sai ya fara kokawa. Ya shaida mini cewa sau uku ’yan sanda na kama shi.”

Ya kara da cewa “An kulle shafin nawa na Facebook, sai na koma ina amfani da shafina na Instagram inda a can ne na hadu da wannan matar muka yi ta zantawa. Sai na shaida mata cewa zan aiko mata da tsarabar tufafi da takalma da agogon hannu masu tsada da kuma Dalar Amurka dubu 500, domin ta zuba mini jari a harkar saye da sayar da gidaje a kasarsu.”

Arikibe ya ce, sai ya aike mata da hotunan karya na kayayyakin da ya yi karyar zai aike mata da su har ma da hounan tulin kudin, sannan ya gamsar da ita cewa ta aike wa wanda zai kai mata sakon da kudin kaiwa. Ya ce, “Na shaida mata cewa na aike mata da kudin ta hannun wani kamfanin aikewa da sakonni amma za ta biya harajin kwastam. Abokina da ke kasar Indonesiya ya yi aiki a matsayin shi ne mai kamfanin aikewa da sakonnin suka kuma yi magana da ita. Da farko an nemi ta biya Dala 800 wanda ta biya nan take. Sai abokin nawa ya kira ta ya ce mata an rike kayayyakin, don haka sai ta biya Dala 2,700 domin a saki kayayyakin. Bayan ta aike masa da karin kudin ne, sai ya bukaci ta sake aikewa da Dala 6,200, ta kuma aike. Da haka dai ya sanya ta yi ta biyan kudaden don a sako kayayyakin, inda sai da ta aike da Dala dubu 75, a ciki ne aka ba ni nawa kason.”