✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan Majalisar Tarayya daga Ogun ya sauya sheka zuwa APC

Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar; Egbado ta Arewa/Imeko Afon ta Jihar Ogun, Jimoh Aremu, ya sauya sheka daga Jam’iyyar ADC zuwa APC mai mulki.…

Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar; Egbado ta Arewa/Imeko Afon ta Jihar Ogun, Jimoh Aremu, ya sauya sheka daga Jam’iyyar ADC zuwa APC mai mulki.

Shugaban Majalisar Wakilatai, Femi Gbajabiamila, ne ya sanar da ficewar a zauren majalisar a zamanta na ranar Laraba.

Aremu ya ce, “Rashin zaman lafiya da rabuwar kai a tsohuwar jam’iyyar tasa ne dalilinsa na yanke shawarar tarkata komatsansa zuwa a APC.

“Zan yi bakin kokarina don tabbatar wa jama’ar mazaba ta ‘yancinsu na gudanar siyasa mai cike da ‘yanci.

“Ina mai tabbatar da jama’ata cewa za su amfana da shiga ta APC,” inji shi