✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan majalisar tarayya daga jihar Kano ya sha da kyar

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Kano ta yi watsi da karar da aka shigar ana bukatar tube dan Majalisar Wakilai mai wakiltar…

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Kano ta yi watsi da karar da aka shigar ana bukatar tube dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Takai/Sumaila, Muhammad Shamsuddeen Bello Danbazau na APC.

A hukuncin da ya yanke, alkalin kotun, Mai Shari’a Lewis Allagoa, ya ce kotun koli ta yanke hukunci a kan karar da dan takarar jam’iyyar PDP Sirajo Idris Kanawa ya shigar inda ya bukaci a tube dan majalisar.

Alkalin ya ce karamar kotu ba ta da hurumin yanke hukunci a kan abin da babbar kotu ta yanke, don haka hukuncin babbar kotun ya take ko wanne hukunci.

Tun da fari dai dan takarar na jam’iyyar PDP ya shigar da kara ne yana neman kotun ta yanke hukunci a kan ko ya dace a bayyana dan takarar da bai tsaya a zaben ‘yan majalisar tarayya na  ranar 23 ga watan Fabarairun shekarar 2019 a matsayin wanda ya lashe zaben, bisa la’akari da sashe na 285 (13) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.

Wanda ya shigar da karar ya kuma bukaci kotu da ta soke takardar shedar da Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta bai wa Dambazau, kana ta tabbatar da mai karar a matsayin wanda ya lashe zaben.

Kalubale

Da yake kalubalantar wannan bukata, lauyan hukumar  INEC Hassan Aliyu ya bukaci kotun ta yi watsi da karar saboda ba ta da madogara, domin  tuni kotun da ke sauraren kararrakin zabe da kotun koli suka yanke hukunci a kai.

Rikici kan kujerar dan majalisar tarayya mai wakiltar Takai/Sumaila ya samo asali ne bayan da tsohon  mai bai wa Shugaba Muhammadu Buhari shawara na musamman  a kan harkokin majalisar,  Abdurahman Kawu Sumaila, ya lashe zaben a karkashin inuwar jam’iyar APC, amma kotun koli ta bai wa hukumar INEC umarnin karbe takardar shaida daga hannun Hon. Sumaila ta kuma bai wa Muhammad Dambazau a matsayinsa na dan takarar jam’iyar bayan ya shigar da kara har zuwa matakin kotun koli.