✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan Majalisar Filato ya rasu ana cikin bikin murnar sake zabensa

Dan Majalisar Dokokin Jihar Filato mai wakiltar Mazabar Pengana da ke Karamar Hukumar Bassa Honarabul Ezekiel Bauda Afon ya rasu a daidai lokacin da ake…

Dan Majalisar Dokokin Jihar Filato mai wakiltar Mazabar Pengana da ke Karamar Hukumar Bassa Honarabul Ezekiel Bauda Afon ya rasu a daidai lokacin da ake tsakiyar bikin murnar sake zabensa karo na biyu a gidansa da ke garin Jos sa’o’i kadan bayan sanar da cewa ya lashe zaben, a ranar Lahadin da ta gabata.

Da yake yi wa wakilinmu karin bayani kan yadda wannan lamari ya faru, wani dan wan marigayin da al’amarin ya faru a idonsa, mai suna Sunday Joshua Bauda ya ce bayan da aka sanar da nasarar marigayin, sai jama’a maza da mata suka zo gidansa aka taru ana ta murna, aka sa kida ana rawa ana cin abinci.

Ya ce a lokacin, marigayin yana cikin gidan yana zaune da wadansu dattawa.

“Yana zaune sai matasarsa ta kawo masa fate sai ya ce a kawo masa shinkafa, yana cikin cin shinkafar a kan kujera, yana hira yana dariya da mutane, sai aka ga ya fadi,” inji shi.

Ya ce suna waje, sai suka ji an ce a rage karar kidan da aka sanya. Can kuma sai aka ce a kashe kayan kidan gaba daya.

Ya ce sai aka fara neman mabudin mota, kafin a je a kawo mabudin mota sai ya ga yaronsa da motoci  uku, sai ya karbi guda daya.

Ya ce suna cikin wannan hali, sai ya ga an riko marigayin aka sanya shi a mota, suka nufi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH), kafin su je asibitn ya rasu a hanya.

Ya ce babu wani rashin lafiya da yake damun marigayin.

Ya kara da cewa gaskiya an yi babban rashi, domin marigayin mutum ne mai hakuri mai son jama’a kuma mai sauraron jama’a a duk inda yake, kuma dukan iyalai da ’yan uwansa suna rataya ne a wuyansa.

Marigayin an zabe shi dan majalisar mazabar Pengana ne a shekarar 2015 a karkashin Jam’iyyar PDP, daga baya ya canja sheka zuwa Jam’iyyar APC, inda aka sake zabensa a kujerar, a zaben da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.

Ya rasu ya bar mata daya da ’ya’ya 4 maza uku mace daya.