Wani dan Majalisar Wakilan Jihar Kentucky da ke kasar Amurka a karkashin Jam’iyyar Repulican, Mista Dan Johnson da ya musanta zargin yin lalata da wata budurwa a gidansa ya mutu a wani abu da ake ganin kashe kansa ya yi a shekaranjiya da daddare.
Mai bincike kan aikata laifuffuka Dabe Billings wanda ya tabbatar da mutuwar dan majalisar mai shekara 57, ya ce Johnson ya mutu sakamakon raunin harbin bindiga guda daya a kan titin Greenwell Ford da ke Mount Washington a Kentucky.
Billings ya ce Johnson ya tsayar da motarsa a karshen wata da ke wurin da babu jama’a, sannan ya fita ya dan taka zuwa gaban motar. Ya ce za a gudanar da bincike a kan gawar a jiya Alhamis, “Kuma zan iya cewa ga alama shi ya kashe kansa,” inji shi.
A bara ce aka zabi Johnson a matsayin dan majalisar jihar lokacin da guguwar nasarar Jam’iyyar Republican take kadawa, lamarin da ya ba jam’iyyar rinjaye a Majalisar Wakilan Kentucky a karo na farko a kusan shekara 100. Ya samu nasara a zaben ne duk da cewa shugabannin jam’iyyarsa sun bukaci ya fice daga takarar bayan wata kafar labarai ta buga wasu rubuce-rubuce da ya yi a shafinsa na Facebook inda ya kwatanta Barack da matarsa Michelle Obama da birrai.
Johnson wanda Faston cocin Heart of Fire Church ne a Jihar Louisbille, ya gabatar da kudirori da dama da suka shafi ’yancin addini da koyar da Baibul a makarantun gwamnati. Sai dai an kwana biyu ba a ji motsinsa ba, sai ranar Litinin da ta gabata, lokacin da Cibiyar Binciken Rahotanni ta Kentucky ta buga wani labara daga wara mace da ta ce, Johnson ya yi mata fyade a dakin wankanta da ke gidansa a shekarar 2013.
Matar ta ce a lokacin ta shaida wa ’yan sandan da suka binciki lamarin, amma suka kashe maganar ba tare da sun kai kotu ba.
A ranar Talata, Johnson ya kira taron manema labarai a harabar cocinsa, inda ya fara da jagorantar abokai da iyalai ga rera wakar maraba da Kirsimeti ta “O Come All Ye Faithful.” Daga nan ya ce zarge-zargen da ake yi masa “karairayi ne” kuma ya ce wani bangare ne na dabarun kawar da masu ra’ayin rikau na Jam’iyyar Republicans daga mulki. Ya kawo misali da dan takarar Sanata na Alabama karkashin jam’iyyar da ya sha kaye Roy Moore, wanda shi ma ake zargi da aikata badala da mata masu yawa.
Sannan daf da karfe 5 na yammacin shekaranjiya Laraba sai Johnson ya tura wani sako a shafinsa na Facebook yana bukatar mutane su dauki nauyin kula da matarsa. Ya rubuta haruffan cewa PTSD “wata cuta ce da za ta dauki rayuwata. Ba zan iya magance ta ba. Ta samu nasara a wannan rayuwa, AMMA SAMANIYA CE GIDANA.” Alamu sun nuna an cire wannan rubuta daga baya.