✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan majalisa ya sha da kyar 1

Makoni biyu da suka gaba, wani jirgin saman yaki  ya kai hari kan tawagar dan majalisar dattijai, Muhammad Ali Ndume. Wannan dan majalisa da ke…

Makoni biyu da suka gaba, wani jirgin saman yaki  ya kai hari kan tawagar dan majalisar dattijai, Muhammad Ali Ndume. Wannan dan majalisa da ke wakiltar Jihar Barno, ya yi nufin kai ziyarar jaje ga al’ummar mazabarsa kan harin kunar bakin wake da ’yan Boko suka kai musu. Ba a dai gano dalilin kai masa wannan harin ba, amma rahotanni suna cewa bama-bamai hudu  aka jefa wa  tawagar danmajalisar dattijai Ndume. Cikin taimakon Allah babu wanda ya same shi, kuma ba a yi asarar rayuka ba. Da hukumomin soja ke mayar da martini, sun bayyana cewa abin da ya auku kuskure ne, kuma shirme ne na matukin jirgin, don haka kuskure ne a yi zaton sojoji sun yi nufin halaka dan majalisar.
Akwai bukatar su bayar da cikakken bayanin da zai sanya tunanin mutane ya daina kai kawo, ta yadda za su samu tabbacin cewa ba dan majalisar aa yi nufin kai wa hari ba, bayan da bama-bamai hudu suka sauko kan tawagarsa, a jerin ’yan motoci kadan. Lallai akwai wannan bukatar, tunda akwai lokacin da aka taba gurfanar da Ndume a gaban kotu, bisa tuhumar  samunsa da hannu a hare-haren kunar bakin wake da ’yan kungiyar Boko Haram ke kaiwa. Har yanzu wannan kara tana nan gaban kotu.
Bayan aukuwar wannan lamari, Jami’an tsaro sun gano cewa bama-baman na rundunar sojan saman Najeriya ne, kuma sai ga shi Ndume ya yi dabara wajen neman mafaka daga harin sojojin da suka kai farmaki kan tawagarsa. Sojojin kasa sun kokarin aike wa da sako ga matukin jirgin, don ankarar da shi irin musifar da ta kusa aukuwa a kasa. dan majalisar dai ya cika da takaici, jin saura kadan da an cutar da abokan tafiyarsa.
Wannan hari ba shi ne na farko da aka taba kaiwa ba. A cikin watan Oktobar bara, an kai hari kan masu bikin aure, inda daga bisani  jami’an soja suka bayar da sanarwar cewa an yi zaton bakin da suka halarci bikin ’yan kunar bakin waken kungiyar boko Haram ne. aukuwar irin wadannan al’amura akwai tambaya a kan kwarewar sojan saman da ke tare da rundunar tsaro ta JTF, ta yadda za su iya fatattakar ’yan kunar bakin wake daga sama.
Kuma wannan na nuni da cewa sojoan sama da ke tare da rundunar tsaro ta JTF, akwai kalubale a gabanta, wajen tantance abubuwan da ke motsi a doron kasa, al’amarin da ke nuni da cewa babu alakar sadarwa a tsakanin jiragen da ke farautar ’yan kunar bakin wake da kuma tashar da ke ba su umarni kan abin da ya kama su tunkara. Farmakin sojan sama ana yin sa ne don tallafa sojojin kasa su auiwatar da aikinsu, ta yadda za samu damar karya lagon abokan gaba cikin kankanen lokaci. Saboda haka ganin yadda ake ta yin kuskuren kai hari ga motocin masu wucewa da mutanen da ke gudanar da harkokinsu, ha rake dauka cewa su ne ’yan kunar bakin wake, wannan na nuni da cewa akwai bukatar a shata iyakar wuraren da ya kamata akai farmaki ta sama a wannan yanki, don shawo kan musifun da ka iya faruwa.
Lallai ya kamata hukumomin soja su yi nazari kan wannan al’amari, ta yadda za su warware matsalar cikin sauri. A zamanin da ake amfani da makamai masu inganci, bai kamata a cewa rundunar sojan saman Najeriya da ke gudanar da aiki a yankin Arewa maso Gabas, za ta dauka masu bikin aure su ne ’yan kunar bakin wake daukee da makamai. Ta kuma iya yiwuwa, dalilin aukuwar wadannan kura-kurai, shi ne, babu na’urorin zamani da ya kamata a yi amfani da su wajen hangen wuraren da za a kai hari, sannan babu wadanda suka kware wajen aiwatar da wasu muhimman ayyuka, don a akwai bukatar nan gaba rundunar tsaro ta JTF ta wanke kanta daga zargi, ta hanyar samar da kayan aikin da ake bukata, sannan jami’anta su samu horon da ya dace, don kaddamar da hare-haren cikin nasara.
An yi asarar rayukan dimbin mutane wadanda ba su ji ba, ba su ga ni ba, a wajen yaki da masu kunar bakin wake, ta hanyar kyale matukan jirgin da ba su samu ingantaccen horo ba, suna hawan jiragen yaki, wadanda babu na’urorin zamani, shi ya sa suke yin mummunar barna a kan mutane. Hanya mafi sauki da za a shawo kan wannan, ita ce hukumomin soja su tabbatar da cewa an samu alakar sadarwa tsakanin rundunonin da ke yaki da kunar bakin wake. Wannan zai iya hadawa da gaskiyar nufi da amana a tsakanin rundunoni ta yadda kowane zai sa hannu akan aikin da kowane sashe ke gudanarwa. Idan aka aiwatar da wannan shirin, to matukin jirgi zai iya tabbatar da hakikanin wurin da ya dace ya kai hari, ko kuma inda bai dace ba, a doron kasa.