✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

dan majalisa ya koka kan watsi da Kogin Hadeja

Sabon dan Majalissar Tarayya daga mazabar Kafin Hausa da Auyo da Hadeja Alhaji Usman Ibrahim Kamfani ya nuna damuwa kan yadda Gwamnatin Tarayya ta yi…

Sabon dan Majalissar Tarayya daga mazabar Kafin Hausa da Auyo da Hadeja Alhaji Usman Ibrahim Kamfani ya nuna damuwa kan yadda Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da kogin Hadeja har ya zama mutanen yankin ba sa iya noma sai zuwa yawon ci-rani.

Alhaji Usman Kamfani ya bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taimaka ya farfado da aikin noman rani a kogin don ci gaban masarautar Hadeja wadda take neman zama koma-baya a harkokin noma.
Ya ce Kogin Hadeja ya toshe saboda babu hanyoyin da ruwa zai wuce zuwa Tafkin Chadi sakamakon yawaitar ciyawar kacala da ta mamaye kogin a yankin Kirikasamma da Birniwa da wani sashi na karamar Hukumar Guri.
dan majalisar ya kara da cewa mafi yawan manoma sun hakura da aikin noman rani saboda kogin ba ya bayar da ruwan da suke bukata kuma da dama sun yi kaura sun koma yankin Chadi saboda ta’adin jan-baki da suka addabi manoman yankin.
Sai ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta samar da kayan aiki a yashe kogin ta yadda ruwa zai samu
ya gudana manoma su samu damar yin aiki a gonakinsu. “Kuma ina kira ga Gwamnatin Tarayya ta taimaka ta kammala aikin ruwa da ta fara a Kogin Auyo wanda manoma suke amfana da shi amma aka yi watsi saboda siyasa,” inji shi.
Usman Kamfani ya ce shugabannin baya sun yi watsi da aikin kogin saboda dalilai na kashin kansu, domin ba sa son ci gaban yankin, inda ya bukaci sabuwar gwamnatin jihar ta samar wa matasa aikin yi musamman a yankin masarautar Hadeja.