✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan Maganan Dutse ya yi bikin cikar shekara Daya a karagar mulki

Dan Maganan Dutse da mai Martaba Sarkin Dutse ya nada a matsayin kakakin fadarsa na musamman Malam Shu’aibu Aliyu Yargaba ya shirya gagarumin hawa domin…

Dan Maganan Dutse da mai Martaba Sarkin Dutse ya nada a matsayin kakakin fadarsa na musamman Malam Shu’aibu Aliyu Yargaba ya shirya gagarumin hawa domin nuna farin cikin kai wa kimanin shekara daya a matsayin Dan Maganan Dutse da Mai martaba Sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhammed Sunusi ya nada shi.

A lokacin hawan da aka yi a ranar Juma’ar da ta gabata, fitattun ‘yan wasan Hausa irinsu Ali Nuhu da Daushe da baba Ari da Bosho da Kabiru Nakongo da sauran al’umma sun mara mi shi baya, sannan manyan mutane sun hau dokin kara.

‘Yan wasan Hausa da ‘ya’yan kungiyar zabi sonka daga jihohin Kano, Jigawa, Sakkwato, Katsina , Kaduna da Adamawa da Bauchi sun halarci Birnin Dutse domin halartar hawan.

Da yake jawabi bayan saukarsa daga kan doki, Cikago ya ce ya gode wa Maimarta Sarkin

Dutse da ya nada shi daya daga cikin hakimansa.

Ya ce matsayin da maimartaba ya ba shi ba karamin matsayi bane a rayuwa, domin duk inda ya shiga a duniya ana ba shi daraja sakamakon matsayin da masarautar dutse ta nada shi. Ya kara da cewa duk da cewa yana aiki a gidan Rediyo, ana jin sunansa, alakarsa da masarauta ita ce ta sa jama’a suka sanshi kuma ya yi fice a duniya.

Hakanan kuma Dan Maganan ya shawarci jama’a da su zama masu bai wa masarauta hadin kai kuma su guji tayar da zaune tsaye musamman a cikin irin wannan lokaci na siyasa. Sannan kuma ya hori matasa da su zauna lafiya su guji shiga bangar siyasa ta hanyar daina amincewa da wasu miyagun ’yan siyasa da suke amfani da su wajen cimma burinsu a siyasance.

Daga karshe sai ya yi kira ga talakawa da su guji yada jita-jita kuma su yi koyi da halayan maimartaba Sarkin Dutse na kaunar zaman lafiya, sannan ya danganta maimartaba Sarki da cewa mutun ne mai son zaman lafiya a cikin jerin Sarakunan Najeriya