✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

dan kwallon Kwaddebuwa ya kamu da ciwon zuciya

Kulob din Al-kadisiyah na Saudiyya ya bayyana cewa daya daga cikin ’yan kwallonsa mai suna Herbe Guy dan asalin Kwaddebuwa Likitoci sun tabbatar ya kamu…

Kulob din Al-kadisiyah na Saudiyya ya bayyana cewa daya daga cikin ’yan kwallonsa mai suna Herbe Guy dan asalin Kwaddebuwa Likitoci sun tabbatar ya kamu da ciwon zuciya kuma tuni aka ba dan kwallon umarnin ya koma gida don ya ci gaba da neman magani.

Rahotanni sun nuna dan kwallon bai san yana da wannan cutar ba har sai da Likitocin kulob din suka yi masa gwaje-gwaje, daga nan ne suka gano yana dauke da cutar sannan suka sanar da mahukunta kulob din halin da ake ciki.

Daraktan kulob din Ghazi Ageri ya ce, Likitocin kulob din ne suka gargade su da kada su kuskukura su sake sanya dan kwallon a wasa bayan an gano yana dauke ne da wata cuta da ta shafi zuciyarsa da hakan kuma ba karasmin hatsari ba ne ya ci gaba da yin wasa a wannan yanayi.  Kan haka ne aka umarci dan kwallon ya koma gida (Kwaddebuwa) don ya nemi magani kafin ya ci gaba da yi wa kulob din kwallo.

Sai dai Daraktan kulob din ya ce za su ci gaba da karfafa wa dan kwallon gwiwa kuma sun sha alwashin ba za su maye gurbinsa da wani ba har sai ya samu sauki kuma ya ci gaba da yin wasa a kulob din.

Herbe Guy, dan shekara 33 ya koma kulob din Al-kadasiyya na Saudiiya ne a shekarar 2011 bayan ya shafe shekara 4 yana tare da wani kulob a Maroko mai suna Ittihad Tanger.  Yana daga cikin ’yan kwallon Kwaddebuwa ’yan kasa da shekara 20 da suka halarci Gasar cin kofin duniya na matasa a shekarar 2003.