✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan Kwallon Enugu Rangers ya koma Sweden

Daya daga cikin ’yan kwallon da suka fi zura kwallaye a raga a kakar wasan da ta wuce, Chisom Egbuchalam, dan kwallon Enugu Rangers kakarsa…

Chisom EgbuchulamDaya daga cikin ’yan kwallon da suka fi zura kwallaye a raga a kakar wasan da ta wuce, Chisom Egbuchalam, dan kwallon Enugu Rangers kakarsa ta yanke saka bayan ya samu nasarar komawa Sweden don buga wa kulob din BK Hacken da ke wasa a gasar rukuni-rukuni na kasar kwallo.


Dan kwallon wanda ya yi yunkurin komawa kulob din Etiole Du Sahel da kulob din Club Africain na Tunisiya a bara amma bai samu nasara ba a yanzu za a iya cewa hakarsa ta cimma ruwa.


A bara Chisom ne ya kasance na biyu a jerin ’yan kwallon da suka fi zura kwalloaye a gasar firimiya ta kasa bayan ya zura kwallaye 13 da hakan ta sa kulob din Enugu Rangers ya samu nasarar lashe gasar firimiya ta kasa a karon farko bayan shekara 32.


Chisom ne da kansa ya bayyana labarin komawa Sweden a shafin zumuntarsa na Twitter da Facebook a ranar Talatar da ta wuce.
Sai dai dan kwallon bai bayyana yawan kudi da kuma tsawon lokacin da ya sanya hannu a kwantaragi ga kulob din na Sweden ba.