Ana cafke wani dan kasuwa kan yunkurin kashe matarsa don ya samu damar sayar da talabijin dinsu ya kara jari a shagonsa a Jihar Bauchi.
Magidancin mai shekaru 35 ya shiga hannu ne bayan ya yi amfani da tabarya wajen dukan matar tasa da nufin kashe.
Rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi ta ce, magidancin, ya shaida wa masu bincike “cewa ya yi niyyar kashe matarsa ne don ya dauki talbijin dinsu ya sayar, ya samu kudi ya kara kaya a shagonsa.”
Kakakin rundunar, Mohammed Ahmed Wakil, ya ce an kai matar Asibitin Kwararru da ke Bauchi domin kulawar da ita a sakamakon munanan raunukan da mijin ya yi mata da tabaryar.
- Kisan ’Yan Mauludi: Bala’in ya yi wa ’yan Arewa yawa —Bello Yabo
- DSS za ta fara kerawa da sayar da jirage marasa matuka
“Bincike na farko ya nuna wanda ake zargin ya amsa tuhumar da ake masa ba tare da wata turjiya ba.
“Ya yi ikirarin cewar ya yi karyar cewa ’yan fashi sun shiga gidansu, shi ne ya shiga dakin da suke kwance da matarsa ya ce mata ta rufe kanta da gyale.
“Sai ya fita ya je ya rufe fuskarsa da mayafi, sannan ya dauko tabarya ya dawo dakin ya fara dukanta da ita,” in ji kakajin rundunar.
Ya ce abin ya faru ne a ranar Asabar, 2 ga watan Disamba, 2023, kuma kwamishinan ’yan sandan ijhar, Auwal Mohammed, ya bayar da umarnin mika wanda ake zargin ga sashen binciken manyan laifuka don zurfafa bincike da kuma gurfanarwa a kotu da zaran an kammala bincike.