✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan Jarida ya mutu yana tattakin zuwa wurin aiki saboda karancin takardun kudi

Jama’a a Najeriya na ci gaba da wahala saboda karancin takardun kudi.

Wani fitaccen dan jarida da ke aiki a gidan rediyon Ibadan, ya riga mu gidan gaskiya a kan hanyarsa ta zuwa wurin aiki a safiyar wannan Asabar din.

Ma’aikacin jaridar wanda aka fi sani da Baba Bintin, ya yanke jiki ne ya fadi matacce kamar yadda wakilinmu ya ruwaito.

Bayanai sun ce lamarin ya faru ne yayin da Baba Bintin ke hanyarsa ta zuwa gidan rediyon Fresh FM, inda zai gabatar da wani shiri tare da wasu takwarorinsa, Komolafe Olaiya da Olalomi Amole a yankin Challenge da ke Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.

Baba Bintin dai ya shahara wajen gabatar da shirin bayyana farashin kayayyaki da ranakun cin kasuwannin yau da kullum a fadin jihar da kewaye.

Rahotanni sun tabbatar da cewa karar kwana ta cimma Baba Bintin yayin da yake tattaki tun daga unguwarsu ta Amuloko zuwa Challenge sanadiyyar rashin tsabar kudi a hannu da zai biya masu ababen hawa na haya.

Jama’a a Najeriya na ci gaba da babatu kan halin kunci da suka shiga tun bayan sauya fasalin takardun kudi da Babban Bankin Kasar CBN ya yi.

CBN dai ya sauya fasalin takardun kudi na N200, da N500 da kuma N1,000 tare da dakatar da amfani da tsofaffin takardun kudin, lamarin da wasu gwamnoni suka kalubalanta a Kotun Koli.

A kan hakan ne Kotun Kolin a farkon wannan wata na Maris ta ba da umarnin ci gaba da amfani da tsoffin takardun kudin har zuwa ranar 31 ga watan Disamba, 2023.

Sai dai har yanzu Gwamnatin Tarayya ta shafa wa idonta kwalli a kan hukuncin, amma dai an samu wasu bankuna da suka soma bai wa abokanan huldarsu tsofaffin takardun kudin kamar yadda Kotun Kolin ta yanke.