Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya A. Sule, ya yi rashin dansa mai suna Hassan A. A Sule.
Sakataren Yada Labarai ga Gwamnan, Ibrahim Addra ne ya tabbatar da rasuwar tasa a sanarwar da ya fitar da safiyar Juma’a.
- Malamai da tsofaffin soji ba sa kwazo a jagoranci —Obasanjo
- NAJERIYA A YAU: Yadda aka tsefe manufofin manyan ’yan takarar Shubancin Najeriya a zaben 2023
“A madadin iyalin Mai Girma Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi A. Sule, na sanar da rasuwar dansa, Hassan A.A Sule, wanda ya rasu ranar Alhamis, 26 ga Janairu, 2023,” in ji sanarwar.
Marigayi Hassan ya bar duniya yana da shekara 36.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa za a yi jana’izar marigayin a garin Gudi, cikin Karamar Hukumar Akwanga da misalin karfe 10:00 na safe a ranar Juma’a.