✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…..dan George Weah ya fara buga wa kulob din PSG kwallo

Rahotanni daga Faransa sun ce dan Shugaban kasar Laberiya mai suna Timothy Weah, mai kimanin shekara 18 ya samu nasarar rattaba hannu a kulob din…

Rahotanni daga Faransa sun ce dan Shugaban kasar Laberiya mai suna Timothy Weah, mai kimanin shekara 18 ya samu nasarar rattaba hannu a kulob din Paris Saint Germain (PSG) na Faransa kuma tuni ya fara yi wa kulob din kwallo.

Kimanin shekara 23 da suka wuce ne Shugaban na Laberiya George Weah ya buga kwallo a kulob din PSG sai ga shi dansa Timothy ya samu nasarar maye gurbinsa a kulob din da hakan ya zama abin tarihi.

A karshen makon jiya ne Timothy ya taimaki kulob din PSG wajen lallasa kulob din Troyes da ci 2-0 a gasar rukunin Faransa (Ligue 1) da hakan ta sa kulob din PSG yake saman teburin gasar kuma ya bayar da tazarar maki 14.

George Weah dai ya yi kwallo ne a kulob din PSG a tsakanin 1992 zuwa 1995 kuma ya samu nasarar zura kwallaye 55 a lokacin da yake buga wa kulob din kwallo.