✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan China: Mahaifiyar Ummita ta bayyana a matsayin shaida ta farko kan kisan ’yarta

Kotun ta zauna ne a ranar Laraba

An ci gaba sauraron shari’ar dan kasar China wato Mista Geng Quanrong a gaban Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 17 da ke zamanta a unguwar Miller Road.

Kotun dai na karkashin jagorancin Mai Shari’a Sunusi Ado Ma’aji.

Ana zargin Mista Geng Quangrong ne da kisan budurwarsa, Ummmulkulsum Buhari, wacce aka fi sani da Ummita.

A zaman kotun na ranar Laraba, lauyoyin gwamnati bisa jagorancin Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano Barista Musa Abdulahi Lawan, sun gabatar da shaidarsu ta farko mai suna Fatima Zubairu mai kimanin shekara 43 wacce ita ce mahaifiya ga Ummita, wanda ake zargin dan kasar Sin din da caccaka mata wuka a ranar 16 ga watan Satumba 2022 wanda hakan ya yi sanadiyar rasuwarta.

Kotu ta tambayi mahaifiyar Ummulkursum ko ta yaya ta san Quarong, inda ta ce ta san shi ne sakamakon zuwa wajen ’yarta da yake yi har gida.

Aminiya ta ruwaito cewa ana cikin yi wa Fatima tambayoyin ne mai shari’a ya tafi hutun muntuna 15.

Muna tare da karin bayani…