✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan Celestine Babayaro ya koma kulob din Newcastle United

Rahotanni sun nuna kocin kulob din Newcastle United da ke Ingila Rafa Benitez ya gayyaci yaron tsohon dan kwallon Najeriya Celestine Babayaro Ryan Hyacinth don…

Rahotanni sun nuna kocin kulob din Newcastle United da ke Ingila Rafa Benitez ya gayyaci yaron tsohon dan kwallon Najeriya Celestine Babayaro Ryan Hyacinth don ya yi wa kulob din kwallo a matakin yara saboda kwazon da ya nuna.

dan Babayaro, Ryan Hyacinth, shi ne Gwarzon dan kwallo a gasar da wata Cibiya da ke karkashin kulob din Newcastle United ta take shiryawa a duk shekara, kuma shi ne ya zama dan kwallon da ya fi yawan zura kwallaye a raga a gasar da hakan ta sa ya yi suna kuma  ya ja hankalin kocin wajen gayyatarsa.

Ryan dai ya taimakawa Firamaren da yake karatu Cambouis Primary School Nothernberland ce wajen lashe kofin da ake wa lakabi da 1892 Foundation Cup da hakan ta sa kocin ya nemi ya koma kulob din don ya ci gaba da samun raino a bangaren yara. 

“Muna bukatar karfafa zumuncin da ke tsakanin kulob din Newcastle ne da kuma al’ummar yankinmu, don haka ne muke shirya irin wannan gasa a duk shekara don zakulo yaran da suke nuna hazaka don mu ci gaba da horar da su a Newcastle United”, inji Benitez.

Celestine Babayaro dai ya taba bugawa kulob din Newcastle United kwallo ne a a tsakanin shekarar 2005 zuwa 2008. Ya buga wa kulob din Anderlech na Beljiyum kwallo a tsakanin shekarar 1994 zuwa 1997 daga nan ya koma Chelsea a tsakanin shekarar 1997 zuwa 2005 daga nan ne ya canza sheka zuwa kulob din Newcastle na Ingila.  Bayan ya bar Ingila ne sai ya koma kulob din Los Angeles Galady na Amurka a shekarar 2008 kuma a shekarar ce ya yi ritaya daga yin kwallo.

Tuni Ryan ya koma kulob din Newcastle don ci gaba da samun horo a bangaren yara.