✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan Argentina ya fasa sayen gida don tafiya kallon Messi a Gasar Cin Kofin Duniya

Ya ce ya gwammace ya je kallon Messi a Qatar da ya sayi gida

A yayin da ya rage kasa da mako biyu a fara Gasar Cin Kofin Duniya, wani dan kasar Argentina ya tattara kudaden da ya tara da niyyar sayen gida don tafiya kasar Qatar ya kalli yadda dan wasan kasar Lionel Messi zai taka leda.

Mutumin, mai suna Emiliano Matrangolo, mazaunin birnin Buenos Aires na kasar, ya ce ya yanke shawarar ce don ya sami zuwa kasar ta Qatar don kallon gwanin nashi.

Emiliano, mai shekara 39 dai yana son zuwa gasar ne don nuna goyon bayansa ga tawagar kasarsa, da kuma dan wasanta, Messi.

Ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, “Shekara hudu na yi ina tarin kudi a kowanne wata don ganin na cika burin nawa.

“Mutum zai fasa yin abubuwa kamar su sayen mota ko gida,” kamar yadda ya shaida a gaban wata katuwar tukubar nama da magoya bayan tawagar suka shirya gabanin tafiya Qatar din.

“Tafiya ce da na jima ina mafarkin yin ta. Mutane da dama za su ce kalle shi, zai kashe kudadensa don tafiya Qatar a maimakon ya fara biyan kudin gida.

“Gaskiya ne mallakar gida abu ne mai kyau, amma ni dai Qatar zan tafi,” inji shi.

Akwai dai yiwuwar wannan gasar cin kofin duniyar ta kasance ita ce wacce Messi, mai shakara 35, zai buga a matsayin ta karshe a wannan watan na Nuwamba.

Kasar ta Argentina dai na da burin ganin ta sake lashe kofin a karo na uku, bayan sau biyun da ta taba yi a shekarun 1974 da 1986.

Bugu da kari, duk da matsin tattalin arziki da tashin farashin kayayyakin da kasar ke fama da su, ’yan kasar na cike da kyakkyawan fatan tafiya don goyon bayan tawagar kasarsu.