A rana ta sili da kofar hanci ga watan Ukkun-Baba na sheklara ta dubu karamin lauje da sili da babban lauje, jaridar Ladarshafi ta ruwaito labarin cewa, Babban Asusun Haurobiyaya umarci daukacin asusu-asusun kasuwanci da su daina ikrarin mallakar damon dukiya. Kuma a cikin makon da ya arce, kafafen watsa batutuwa a Haurobiya, musamma ma jaridu un bijiro da yadda hukumar kula da fanshon ’yan kwadago zai shiga cikin kasuwar hada-hadar hannun jari. Kai wannan al’amari uya kai jaridar Dalilin-taronsu ta yi watsattsaken ra’ayinta kan hadin gwiwar kasuwar da hukumar fanshon, ta yadda za a hana yi wa tsofaffin ’yan kwadago fanco a rayuwarsu.
Wadannan batutuwa da aka bijiro da su dangane damin Hauro a kasar Haurobiya, na fasko cewa, damon dukiya ce, amma ta dokin-wuya. Domin irin wannan tarin ’yan matsabbai da ke dankare a asusu-asusun kasuwancin kasar Haurobiya, yawancinsu an daina mu’amala da su, saboda yawancin masu dukoya sun kwanta dama, a wani yanayin kuwa sun fice daga kasar.
Batun dukiyar ’yan kwadago ta fansho kuwa da ake niyyar tsomata a cikin tsomomuwar kasuwar hada-hadar ririta jinjirin jaririn jari, ita ma sai an yi taka-tsantsan, don gudun kada a yi facaka ko a finciko ficika, yadda tayar tafiyar rayuwar tsofaffin ’yan kwadago za ta yi fanco, alhali babu mai faci.
Jaridar Dalilin-taronsu, ta yi na’am da wannan tsari da ake yunkurin bullo da shi, amma ta bukaci a yi takatsantsan, don gudun kada a salwantar da dimbin dukiyar al’umma a duk lokacin da kasuwa ta ruguzo, musamman in an yi la’akari da abin da ya auku a shekara ta dubu karamin lauje da madambaci.
Kusan kowa a kasar nan yana da masaniya kan yadda masu handama da babakere suka dibgo basussukan wuni-wuni, irin na ’yan uwan da ba su da wani, hart a kai ga an yi rugu-rugu da asusu-asusunmu. A yau in ban da Giwa mni mangalar Hauro da Uba mai tarairayar dukiyar ’ya’yansa da Zannin kudi da Asusun assasa asarar Hauro (wanda idan aka ambaci sunansa, sai ka kamar korar kaza, wato “ass!ass!), su kadcai ke tsaye da kafafunsu. Sauran kuwa an cefanar da su, illa ’yan kadan da ke karkashin kulawar Kamfanin Aman-kunu (wanda aka kirkiro shi don sayen asara da ririta riba).
Lallai akwai bukatar mahukunta su himmatu wajen kashe wa al’umma karsashin fatara da kwance talalar talauci, har ta kai ga kowa ya samu jarin fatauci. Tunda an yi bikin ‘’yanci babu ’yan cici, sai a rika yi mana kyakkyawan hukunci, don mu rika ganin mahukunta da mutunci. Kun ga ke nan dole a kauce wa almubazzaranci da sakaci da lalaci. Kada mu bari a yi mana wa-ka-ci-ka tashi.
Batu na ingarman karfen karafa, akwai bukatar a tattara dimbin masanan tattali, su gana da ’yan kwadago masu neman kadago kan yadda za a sarrafa damin Hauro tiren-taliuya kofar hanci da zagaye. Sannan atsakuro damon dukiya da ta yi likimo a asusu-asusun kasuwancin kasar nan a cakuda su wajen aiwatar da duk wata hada-hada da za ta kawo wa al’umma fa’ida.
Kuma na taba ji daga bakin wani jami’in hukuma da muka saba zama da shi a teburin mai shayi, inda ya bayyana cewa Gwamnatin Baban masu Burin-huriyya na shirin aiwatar da wani tsari da zai tabbatar da cewa, duk wani dan kwadago da ya tara Hauro malala gashin tunkiya a asusunsa/tan a fansho, to za a nemi asusun samar da matsugunni ya samar masa/mata da akurki. Wannan batu na jami’in hukuma idan har ya tabbata, ai shi ke nan, ba sai mutum ya ririta tayar barin kwadago ba, zai iya amfana da ’yan matsabbansa.
’Yan makaranta, mu himmatu wajen jawo hankalin Gwamnatin Tarairayar Haurobiyawa da ta himmatu ka’in da na’in wajen sarrafa waccan damon dukiya, tun kafin ta zma dokin-\wuya, har ta kai ga wasu sun Ankara da ita, su kuma yi mata sabi-zarcem, wato dai su samfe da ita. Don haka ya zama wajibi a bullo da wasu managartan hanyoyinm da za su bai wa Haurobiyawa tabbacin cin gajiyar abin da suka tara lokacin da suke fafutikar neman kadago da kuruciyarsu.
Uwa-uba, idan masu damon dukiya sun bayyana, to a fito da tsarin tantance su, ta yadda za a bioya su dukiyarsu da ta yi likimo. Idan kuwa ba su bayyana ba, to a tuntubi masana, musamman malaman addini, su yi bayani yadda za a yi da ita. Kuma duk mai ajiya a daukacin asusu-asusun kasuwancin kasar nan wajibi ne ya bayar da cikakken bayanin matsugunninsa, ta yadda ko bayana, za a iya danka tarinsa a hannun magadansa, tun kafin ya auka hanna magabta masu kwashi-kwaraf da dukiyar al’umma.
Da zarar hukuma ta aiwatar da shawarar da makarantar Dodorido ta bijiro da ita, to tabbas ’yan kwadago za su samu masalaha a rayuwarsu, kuma hukuma za ta samu saukin farautar samarin-kusu da ’yan matan jaba da ke yin sabi-zarce da dukiyar al’umma, har ma su tatuke lalitar hukuma. Ina fatan wannan batu ya bazu a shafukan Balon-faranti da Faffale-dalili da sauran mujallu da makalutun makalun jaridu, ta yadda kowa zai fasko jirgin masu niyyar tsoma dukiyar ’yan kwadago a cikin tsamiyar tsimin arziki, ta yadda za mu kira dukiyarmu ‘damon dukiyar dokin alfasnu, amma aikata sabanin haka na iya sanyawa a ci gaba da kallonta a matsayin ‘Damon dukiyar dokin-wuya,” wato dai yadda masu yaren Hau-hau ke furtawa, ‘ga dundume kururu, ga kwanan ’yar Babban Birnin Jihar Zaman-fara.’
Damon dukiyar dokin-wuya
A rana ta sili da kofar hanci ga watan Ukkun-Baba na sheklara ta dubu karamin lauje da sili da babban lauje, jaridar Ladarshafi ta ruwaito…