✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Damisa ta hana mazaunan kauyukan Indiya sakat

Dubban mazauna kauyuka a kasar Indiya, sun yi gudun ceton rai, bayan da wata damisa ta balle, ta kuma halaka mutum bakwai, al’amarin da ya…

Dubban mazauna kauyuka a kasar Indiya, sun yi gudun ceton rai, bayan da wata damisa ta balle, ta kuma halaka mutum bakwai, al’amarin da ya kai ga an kulle makarantu da wurin shakatawa.
Maharba sun shiga farautar wannan damisa, wadda take yawon neman abinci a nisan kilomita 80 daga Jihar Uttar Pradesh.
Wani jami’in kula da gandun daji, Rupak De, ya bayyana cewa, “damisar na ta kai kawo ne saboda rashin abinci.
A bara ma an samu rahoton irin wannan damisar da ta halaka mutane. Mafarauta sun ce suna da tabbacin tana nan a cikin wurin shakatawa na kasa, mai lakabin Jim Corbett
Sai dai kuma, wata mai fafutikare kare hakkin namun daji, ’yar majalisar kasar, Meneka Gandhi, ta roki hukumomin yankin kada su harbi wannan damisar. A cikin wata wasika da ta aike wa gwamnati, ta bayyana cewa dabbara tana kai wa mutane hari ne saboda yunwa, kuma za ta bai wa jama’a kariya da zarar an mayar da ita muhallin da ya dace da ita.