✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dambatta ya samu karin lambar yabo

Yakubu Musa Mataimaki na Musamman ga Farfesa Dambatta ya yi tsokaci kan yadda karin bunkasar shiga Intanet ta Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) a karkashin…

Yakubu Musa Mataimaki na Musamman ga Farfesa Dambatta ya yi tsokaci kan yadda karin bunkasar shiga Intanet ta Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) a karkashin jagorancin Shugaban Hukumar NCC, Farfesa Umar Garba Dambatta ta janyo karramawa ta musamman daga jiharsa ta Kano.

Farfesa Umar Garba Dambatta, Shugaban Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) ya sha samun lambar yabo. Tun kafin ya zama babban mai sanya ido na babbar kasuwar sadarwa ta Nahiyar Afirka, Farfesan Injiniyan Sadarwa ya karbi lambobin yabo da takardun shaidar girmamawa daban-daban har kimanin 18.

Wadannan lambobi sun isa duk wani wanda ya cimma wani matsayi ya yi alfahari da su har ga Dambatta da ya cimma buri masu yawa wanda ya zo Hukumar NCC yayin da take yunwar samun nasara.

Da farko matakan da ya dauka su ne suka janyo hankalin duniya ga hukumar. Ya fara bayar da mamaki yayin kaddamar da turbar da hukumar za ta bi. Kuma aiwatar da ajandoji takwas da ya yi ya janyo yabo daga kusa da nesa.

Daga cikin lambobin yabon har da wacce Cibiyar Injiniyoyi ta Najeriya (NAE) wacce ita ce kololuwar inuwar da ta hada kungiyoyin injiniyoya ta kasa ta ba shi da kuma digirin girmamawa na kimiyya da Jami’ar Jos ta ba shi.

Mujallar Tell Magazine ta ba shi lambar yabo ta Babban Jami’in Gudanarwa na Shekara haka ma Mujallar African Leadership ta ba shi mai sanya ido na shekara haka ma an ba shi lambar yabo ta mutum na musamman a harkar sadarwa na shekara a taron bayar da kayaututtuka ta kungiyar masu hada-hadar tarho ta Najeriya da lambar yabo a matsayin mutumin da ya fi fice na shekarar 2017 da Cibiyar Bayar da Kyaututtuka da Kirkira (NTITA) ta ba shi.

Haka kazalika, shi ne fitaccen mutum na shekarar 2018 da Cibiyar Bayar da Kyaututtukan Hada-Hadar Tarho da Kirkira ta Najeriya ta ba shi da kuma kyautar ma’aikacin gwamnati abin bayar da misali na shekarar 2017 ta Jaridar Authority da kuma lambar yabo a matsayin Babban Jami’i mafi kazar-kazar na shekara da kungiyar manema labarai ta Majalisar Wakilai ta ba shi a shekarar 2018.

A bangaren hukumar, Hukumar NCC a karkashin jagorancinsa ta samu lambar yabo ta Turai a matsayin hukumar sadarwa da ta fi kowace a shekarar 2016 sannan ta samu lambar yabo a birnin Buressels da ke kasar Beljiyum a matsayin hukumar da ta fi kowace cimma nasarar ingancin aiki da cibiyar ingancin bincike ta Turai ta bayar a shekarar 2017 da kuma lambar yabon da Hukumar Garambawul din aikin gwamnati ta ba ta.

Haka ma jaridar Leadership ta bai wa Hukumar NCC Lambar yabo a matsayin ma’aikatar gwamnati ta shekarar 2017 da wasu kyaututtukan yabo masu yawa.

Karramawa daga gida tana da matsayi na musamman a zuciya. Ita ce kyautar da ya samu ta sanya ido a karshen makon jiya a birnin Kano. Hakika tana da muhimmanci mai yawa saboda ta zo ne daga kungiyar da Dambata yake da alaka da ita wato Kungiyar Injiniyoyi ta Najeriya reshen Kabuga.

Yayin da yake ganawa da manema labarai a ofishin kungiyar da ke Kano a daren bikin bayar da kyaututtukan na shekarar 2019, ya ce “Na yi farin ciki. Wannan kyauta ce da za mu yi hanzarin amincewa da ita. Muna tantance kyaututtukan da ake ba mu. Akwai wadanda muka ki amincewa da su.”

A matsayina na daya daga cikin masu taimaka masa da ke cikin tantancewar, na san muna mutukar samun kyaututtuka inda muka amince da kashi 30 cikin 100 na kyaututtukan da aka ba mu.

Yayin da yake bayyana lambar yabon da ya samu daga reshen Kabuga a matsayin ta musamman, Shugaban NCC ya bayyana cewa ya taba zama shugaban kungiyar.

“Reshen Kano ne ya samar da reshen Kabuga da na Wudil, wuraren da nake da alaka da su. A garin Wudil na yi sakandare dina kuma Unguwar Kabuga shi ne inda nake zuwa kullum da safe in gabatar da lacca a sabon mazaunin Jami’ar Bayero da ke Kano  a sawon shekara 30 da suka gabata’,’ inji shi

Yayin da yake jawabi kan bayanin da aka yi a kan Dambatta a taron, Shugaban Reshen, Farfesa O.A.U. Uche ya bayyana irin nasarar da Dambatta ya samu a bangaren shiga yanar gizo a kasa baki daya.

Idan za a iya tunawa a kokarin cimma iyakar kashi 30 cikin 100 na shiga yanar gizo a karshen shekarar da ta gabata, akwai damuwa sosai cewa cimma iyakar ba zai yiwu ba. Ba wai kawai cimma iyakar Najeriya ta yi ba har ma ta wuce iyakar a watan Disamban shekarar da ta gabata, yanzu damar samun shiga Intanet ta kai kashi 33 cikin 100.

Wannan ne dalilin da ya sa ya bayyana shirin hukumar na cimma duk wata iyaka da Gwamnatin Tarayya ta sanya mata.

Dadin-dadawa bai wa kamfanonin Infracos lasisin sanya kayayyakin aikin samar da yanar gizo a kananan hukumomi 774 na kasar nan ya bayyana irin shirin da ya yi da kuma sauke nauyin da aka dora masa.

Yakubu Musa shi ne Mataimaki na Musamman Mai Kula da Harkokin Watsa Labarai na Shugaban Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC). Ya rubuto wannan makala ce daga Abuja