Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomi ta NULGE ta yi gargadi cewa kokarin da Gwamnatin Kaduna ke ya na cin zarafin shugabannin NLC kan yajin aikin da suka shiga na iya tsayar da al’amura a Najeriya.
Shugaban NULGE, Kungiyar Ambali Olatunji ne, ya yi wannan gargadi ne yayin ganawarsu da tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai, Ike Ekweremadu, ranar Laraba a Abuja.
- ’Yan daba sun kai wa ’yan kwadago samame a Kaduna
- NECO ta dage jarabawar NCE
- Daga Laraba: Sharar Fage
- ’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda 9 a Habasha
“Kowa yana sane da abin da ke faruwa a Kaduna, in har ba dauki matakin gaggawa ba abun zai zama babba,” inji Olatunji.
Ya roki Ekweremadu kan ya tabbatar da cewa Majalisa ta shiga cikin lamarin ta taka wa El-Rufai burki kan abin da ya kira mulkin kama karya a Jihar Kaduna.
Tun a ranar Litinin NLC ta shiga yajin aiki tare da gudanar da zanga-zangar lumana kan korar da Gwamnatin El-Rufai ta yi wa dubban ma’aikata.
A ranar Talata Aminiya ta rawaito yadda El-Rufai ya bayyana neman Ayuba Wabba da wasu shugabannin kungiyar kwadago na kasa ruwa a jallo kan shirya yajin aikin.
A ranar Talatar wasu ’yan daba suka tarwatsa zanga-zangar NLC da a kan titunan garin Kaduna.