✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dambaruwar NIN: MTN ya kulle dukkanin ofishinsa a Najeriya

MTN ya ɗauki matakin ne bayan yadda aka fara kai wa ofishoshinsa hari.

Kamfanin Sadarwa na MTN ya rufe dukkanin ofisoshinsa da sauran cibiyoyinsa da ke faɗin Najeriya, biyo bayan dambaruwar rufe layukan mutane.

Kamfanin ya sanar da haka ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a safiyar Talata.

MTN ya ce: “Abokan ciniki, a lura mun rufe dukkanin ofisoshinmu a faɗin ƙasar nab, za su kasance a rufe yau, 30 ga watan Yuli 2024.”

Wannan ya biyo bayan koke-koken wasu daga cikin masu amfani da layukan kamfanin a faɗin ƙasar bayan da kamfanin ya rufe musu layuka a ranar Lahadi.

Wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta ya nuna yadda wasu fusatattun kwastomomi suka karya ƙarfen wani ofis ɗin MTN don nuna fushinsu kan rufe layukansu da kamfanin ya yi.

Bidiyon ya nuna yadda kwastomomin MTN suka lalata ofishin kamfanin sadarwa saboda rufe layukansu sakamakon gaza haɗa lambar shaidarsu ta ɗan ƙasa (NIN) da layukansu.

A ranar Litinin, Aminiya ta gano yadda kwastomomi suka yi wa ofishin MTN cikar ƙwari da nufin buɗe musu layukansu.

Biyo bayan koke-koken jama’a, Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), ta umarci dukkanin kamfanonin sadarwa da su sake buɗe layukan mutane da suka rufe.

NCC, a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, ta ce ta yanke wannan shawarar ne saboda bai wa kwastomomi fifiko da muhimmanci.