✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalori ya taya Musulmi murnar bikin Maulidi

Dalori yai kira ga al’ummar Musulmi da su yi amfanin lokacin gunarda bukuwan Maulidi wajen yi wa kasa addu’a musamman ’yan uwansu da ambaliyar ruwa…

Mataomakin shugan jam’iyyar APC mai kula da shiyyar Arewa, Hon. Ali Bukar Dalori ya taya al’ummar Musulman Najeriya murna bikin Mauludi.

Dalori ya ce 12 ga watan Rabi’ul Awwal ita ce ranar da aka haifi Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (SAW), yana mai cewa akwai bukatar Musulmi su yi koyi da shi da dabi’unsa.

Haka zalika Dalori yai kira ga al’ummar Musulmi da su yi amfanin lokacin gunarda bukuwan Maulidi wajen yi wa kasa addu’a musamman ’yan uwansu da ambaliyar ruwa ta shafa a Maidugu.

Dalori ya ce, “Muyi amfani da darusan da ke cikin bukuwan Maulidi musamman wajen koyi dabi’o’in Annabin tsira Sallallahu Alaihi Wasallam.

“Ina mana nasiha da mu yi amfani da wannan lokai na bukuwan Maulidi da yi wa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri.”