✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dallas Cowboy ce kungiyar kwallo mafi dukiya a duniya

Mujallar Forbes ta bayyana kungiyar kwallon kafa da ake yi a Amurka mai suna Dallas Cowboy a matsayin wadda ta fi kowace kungiyar kwallon kafa…

Mujallar Forbes ta bayyana kungiyar kwallon kafa da ake yi a Amurka mai suna Dallas Cowboy a matsayin wadda ta fi kowace kungiyar kwallon kafa dukiya a duniya a bana.
kungiyar Dallas Cowboy ta zo ta daya ce da dukiyar da ta kai Fam biliyan uku da miliyan uku (kimanin Naira tiriliyan daya da biliyan 485) kamar yadda gidan rediyon BBC ya ruwaito.
Wannan ne karo na farko da wata kungiyar kwallo da ba ta ainihin kwallon kafa ba da ke buga tamola da ta haye matsayi na farko, tun lokacin da mujallar Forbes ta fara fitar da kungiyoyin kwallon kafa da suka fi yawan dukiya a duniya a shekarar 2011.
kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta koma matsayin ta biyar a jerin kungiyoyin kwallon kafa na duniya da suka fi dukiya. An kiyasta cewa Man. United wadda ta taba haye matsayi na daya a shekarar 2011 da 2012 tana da kadarorin da suka kai Fam biliyan biyu da miliyan 52, (kimanin Naira tiriliyan 1 da biliyan 134).
Real Madrid ce ta biyu da dukiyar da ta kai Fam biliyan biyu da miliyan 65, (kimanin Naira tirilyan 1 da biliyan 246 da miliyan 500) sai Barcelona ta uku da Fam biliyan biyu da miliyan 69, (kimanin Naira tiriliyan 1 da biliyan 210 da miliyan 500).
Arsenal tana mataki na 23 a jerin kungiyoyin kwallon kafa masu dukiya a duniya, sai Manchester City da ke mataki na 28, Chelsea ta 36 yayin da Liberpool ke mataki ta 41.