Babban Shehin Darikar, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya ce ya jagoranci hawan Idin Karamar Sallah a ranar Laraba ne bayan samun tabbacin ganin jinjirin watan Shawwal a ranar Talata.
Shehin malamin ya yi bayanin ne bayan saukowa daga sallar idin da aka gudanar a gidansa da ke Bauchi a safiyar Talata.
- Sallah Karama: Abubuwan da ya kamata a aika
- Zakatul Fidr: Yadda ake fitar da Zakkar Kono
- Badakar Naira Biliyan 165: PDP ta bukaci Buhari ya tsige Ministan Sufuri
- Kungiyar Dattawan Arewa ta bukaci Majalisa ta tsige Buhari
“Dangane da wannan labarai na cewa wata ya tabbatar, abin da aka ce adalai guda biyu idan sun gani ya isar ma jama’a, ko kuma jama’a masu yawa idan sun ga watan,” inji shi.
Sai dai kuma Idin da shehin da dubban mabiyansa suka gudanar ta saba umarnin Sarkin Musulumi na cewa ranar Alhamis za a yi Karamar Sallah bayan an sha ruwan azumi na 30 a ranar Laraba, saboda ba a ga wata a ranar Talatar ba.
Amma ya yi bayani cewa “An ga wata [ranar Talata] a wurare irin su Gombe da Gadau da kuma Kebbi,” kuma mutanen da suka ga watan “saboda suna da yawa,” kuma ba shi da ikon karyata mutanen da suka tabbatar da ganin watan.
“Shi ya sa yanzu muka zo muka gudanar da sallar Idi domin watan Ramadana ya kare, watan Shawwal ya shigo,” inji shi
Ya yi jawabin ne bayan saukowa daga sallar idin da dansa, Tijjani Dahiru Bauchi ya yi limanci, shi shehin malamin ya kasance a cikin mamu.