Yawancin ’yan matan da suke so su auri mai mata suna gudun saurayi ne saboda gajon hakuri da kuma gudun wahala a ra’ayin wata matar aure marubuciya, kuma malamar makaranta ’yar Kano, Aisha B. Umar.
Yawancin samari ba su da kudi, yanzu suke fafutukar gina rayuwar, da kokarin fuskantar inda ta dosa, rashin gidan kai na gani na fada, rashin mota, kokarin tallafawa iyaye da kanne, malejin rayuwa, idan aikin gwamnati ake yi yanzu aka fara, sai an kai akalla shekara 15 zuwa 20 kafin a fara daukar wani albashi mai tsoka, to ga wanda ma yake da aikin kenan.
- Wata mata ta kona al’aurar mijinta
- Ganawar Sheikh Gumi da ’yan bindigar Neja cikin hotuna
- Coronavirus ta kashe karin mutum 16 a Najeriya — NCDC
Idan yana daukar albashin dubu dari, haka zaku raba tsakanin biyan kudin haya, kudin zuwa asibiti (don ma Allah ya taimakeki kin zo a zamanin da ake da tsarin inshorar lafiya, ciyar da ke da iyayensa, kudin makarantar kannensa, da tsarabe-tsarabe na yau da kullum da sauransu.
Ga uwa uba rashin kwarewa a kan shi kanshi auren, zafin kai irin na matashi, dokoki kala-kala, saurin fushi da hidindimu da su ka yi masa yawa, ga rashin gogewa wajen mu’amala da mace da halayenta, SABODA SHI AURE, KOYONSA AKE!
Wasu ’yan matan kuma da yawa sun kai lokacin da sun fi karfin saurayi, samari ba za su aure su ba, watakila shekaru da budewar ido su jawo mata haka, sannan su ma za su fi son wanda ba zai matsa musu ko takura musu ba, don haka gwara mai mata saboda su ci gaba da rayuwarsu yadda suke so kuma suka tsara, babu sa ido ballatana shata musu dokoki.
Wasu matan da yawa inda suke aiki ma sai a tara samari dari da basa daukar rabin albashin da suke dauka, to suma sun san idan suka ce tilas sai saurayi sun yaudari kan su ne, don masu iya magana na cewa daidai ruwa daidai tsaki.
Wadannan dalilan da yawa da ma wasu, musamman na farko sun sa ’yan mata yanzu Allah-Allah suke su hango wani babban ma’aikacin gwamnati, ko wani matashin dan kasuwa da ya gawurta, ko wanda dai ya fara kama kasa a wajen aikinsa su yi caraf da shi.
Saboda dama ’yan mata suna gudun waccen wahalar ta auren saurayi mai fafutukar gina rayuwa, inda da yawansu ke ganin mai hannu da shuni zai mata gida da mota da lefe na gani na fada sannan a kaita asibiti mai kyau idan ta tashi haihuwa.
Amma fa da yawa ba sa iya jure halin mai mata, so suke sai ya bar iyalinsa ya kama hira da ke. Hajiya, kin manta matar da ta aure shi a irin waccen wahalar da kike gudu a yanzu?
Baki san cewa komai nasa a yanzu nata bane, bare wata aba waya da har kike so sai an mata iyaka da wayar mijinta?
Duk wata kwalliya ta duniyar nan ta yi masa, duk wata tarairaya da girki mai dadi an dafa masa ya ci kafin naki, duk wata shagwaba babu irin wacce ba a yi masa ba, duk wani doki da farinciki na ’ya’yan da za ki haifa an haifa masa.
Babu wata hanya da za ki tallafa wajen gina rayuwarsa saboda rayuwarsa ta gama ginuwa da wata da bata tsoraci talauci ba.
Ke kawai kin zo ki sha romon dabgen da aka dade ana bararrakawa da wata ne, don haka shawara a nan sai ki bi a hankali.
Yana da wahala a yanzu ki samu mijin da matarsa ta fari ba ta zame masa takalmin kaza mutu ka raba ba, don haka ke za ki zamo zabinsa na biyu ce har abada, kuma kin sani.
Sai dai ko shakka babu karin aure ba laifi ba ne, akwai shekarun da idan suka ja, namiji kan bukaci wata macen ba wai wata abokiyar rayuwar ba wadda daman yana da ita, wadda suka koyi aure kuma suka iya shi tare.
Allah ya bawa masu kyakkyawar niyya game da aure abokan rayuwa na gari.