Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta karyata cewa gwamnatoci sun boye kayan tallafin abincin COVID-19 da Gwamnatin Tarayya ta bayar su raba wa mabukata.
Kungiyar ta ce ta gwamnonin sun adana kayan ne domin rabawa a lokacin da ya fi dacewa da nufin inganta rayuwar mabukata.
- ‘Gwamnati ba ta ce gwamnoni su jibge kayan tallafi a rumbuna ba’
- An bukaci Gwamnati ta bankado ma’aikatun da ke rike kayan tallafi
- Masu zanga-zanga sun daka wa kayan tallafin COVID-19 wawa
- Bata-gari sun yashe rumbunan kamfanoni a Abuja
“Muna alhinin wadanda suka rasu a zanga-zangar #EndSARS sannan muna kira da a zauna lafiya.
“Kungiyar gwamnonin Najeriya na sanar da jama’a cewa kayan tallafin abinci da aka yashe a jihar Legas da wasu jihohi na jama’a ne musamman mabukata.
“Duk wani labarin da ake yadawa cewa an karkatar da kayan ne domin biyan bukatar wasu, ba gaskiya ba ne.
“Wasu daga cikin jihohin kasar nan har yanzu suna da kayan tallafin a rumbunansu domin raba su a lokacin da ya dace”, cewar kakakin NGG Abudulrazaque Bello-Barkindo.
Kungiyar gwamnonin ta kara da cewa babu wata jiha da ta boye kayan tallafin domin wata manufa ta daban.
Sannan kungiyar ta tabbatar wa wadanda suka ba da gudummawar cewa gwamnatocin jiha ne ke da alhakin kula da su kafin a yi wawar su a wasu jihohi.
Idan ba manta ba Gwamnatin Tarayya ta ce ba ta ba gwamnoni da Ministan Birnin Tarayya umarnin jibge kayan tallafin su ki raba wa jama’a ba.
Wata majiya a Kwamitin Rabon Kayan Tallafin ga jihohi ce ta tabbatarwa da Aminiya cewa ba Gwamnatin Tarayya ce ta ce gwamnonin su ajiye kayan ba.
Tun ranar Larabar makon jiya ne dai mutane a jihohi ke ta fakewa da zanga-zangar #EndSARS suna fasa rumbunan ajiyar kayan a jihohinsu suna kwashe kayan abincin da duk abin da idanunsu suka yi arba da shi.
Hakan dai ya sa jihohi da dama kokarin kawo dalilan abin da ya hana su raba wa al’ummar jihohinsu tallafin tun a wancan lokacin.
Ya zuwa yanzu dai Fadar Shugaban Kasa da Ma’aikatar Jinkai da Agajin Gagggawa sun ki cewa uffan kan ko gwamnonin jihohi sun boye kayan ne da gangan ko kuma a’a.
A baya dai mutane da dama sun yi ta zargin gwamnatin tarayya kan batun rabon kayan da ta ce ta rabawa jihohin.