Ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar NNPP a Zaɓen 2023, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce la’akari da yanayin da ake ciki a Nijeriya, tura ta kai bango saboda haka tilas ne ’yan ƙasar su miƙe tsaye domin neman sauyin shugabanci a Zaɓen 2027.
Kwankwaso ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a yayin da yake karɓar dimbin mambobin jam’iyyar APC da suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar NNPP a Jihar Kano.
- Gwamna Sule ya ’yantar da fursunoni 12 a Nasarawa
- Ambaliyar Maiduguri: Al’ummar Yarbawa Na Neman Agaji
Aminiya ta ruwaito cewa, Kwankwaso ya karɓi ’ya’yan jam’iyyar APC da suka sauya sheƙar ne daga ƙananan hukumomin Dala da Kiru da Gwale a gidansa da ke Miller Road a Kano.
A cewarsa, “’Yan Nijeriya musamman ma ’yan Arewa sun sha baƙar wahala saboda haka babu wani matsin lamba ko barazana da za ta sa su sauya ra’ayinsu.
“Ya kamata ’yan Nijeriya su sake tunani kan yanayin da ƙasar ke ciki a halin yanzu, saboda ta bayyana ƙarara cewa gwamnatin APC ba ta tare da talakawa.
“Yanzu ta nuna cewa duk da shirinsu [Gwamnatin APC] na amfani da jami’an tsaro da INEC a zaɓe mai zuwa, hakan ba zai yiwu ba saboda ’yan Nijeriya sun kawo wuya kuma tabbas za su yi fafutukar kawo sauyi.”
Tsohon Gwamnan na Jihar Kano ya kuma bayyana kaɗawar guguwar sauyin sheƙa a matsayin tarihi, inda ya bayyana cewa tururuwar da ake yi wajen shiga jam’iyyar NNPP a ƙananan hukumomin Dala da Kiru da Gwale da kuma Dawakin Tofa, ya nuna tubalin da jam’iyyar APC a waɗannan wuraren ya rushe.