✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa nake fitar da albam biyu duk shekara – Nura M Inuwa

Nura M. Inuwa yana daya daga cikin mawakan da duniyar fina-finan Hausa ta Kannywood take bugun kirji da su, inda baya ga wakokin fina-finai da…

Nura M. Inuwa yana daya daga cikin mawakan da duniyar fina-finan Hausa ta Kannywood take bugun kirji da su, inda baya ga wakokin fina-finai da yake yi, yana kuma shirya fina-finai masu dauke da dimbin sakonni. A hirar da Aminiya da shi a kwanakin baya da ya zo Jos, ya bayyana nasarar da ya samu a shekarar da ta gabata, kalubalen da yake fuskanta da kuma dalilin da ya sa yake fitar da albam biyu duk shekara. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

 

Yanzu ga shi mun shiga shekarar 2018, yaya za ka kwatanta nasarar da ka samu a bangaren sana’arka ta waka da kuma shirya fina-finai?

Alhamdulillahi, abin da zan kwatanta a shekarar da ta gabata a gare ni shi ne, shekara ce ta musamman, dalilin da ya sa haka kuwa shi ne, na samu canje-canje a rayuwata, na ga wadansu abubuwa na daban, wadda dole in ce mata ta musamman, kama daga kan ayyukana zuwa rayuwata.

Ko akwai wani canji na musamman da za ka ce ga shi ka samu a shekarar 2017?

Canjin farko dai shi ne, a da ni kadai ne nake rayuwata, ban da nauyin kowa, daga na tashi na yi wanka, sai in wuce wajen aiki, inda kuma cikin ikon Ubangiji sai Ya kawo abokiyar zama, wadda tana daga cikin canjin da na samu kaina a cikinsa. 

Ta bangaren fim ma sai godiya, domin idan ka ga irin fina-finan da muke yi, za a ga akwai canji na yanayin kasuwanci a masana’antar, amma fina-finan kamfaninmu daidai gwargwado dai in an yi to ana saya, duk da cewa mun san mutane suna bibiyar irin abubuwan da muke yi masu ma’ana, shi ya sa kusan suke rububin fina-finanmu duk da yanayin da kasuwar take ciki.

Yawancin shafinka na Instagram za a ga kana sanya hotunanka da kananan yara, ko me ya jawo hakan?

A to, gaskiya halittata ce a haka, ina da son yara tun a baya tun kafin yanzu; yanzu abin da ya sa ya fito fili ake yawan ganin hakan, shi ne, dalilin social media, ita ta sa a da idan ina yi babu wanda ya sani, saboda haka ba a san ni da son yaran ba, sai dai wadanda suke tare da ni, amma saboda social media duk motsina za a ga na yi hoto da yara na sanya, abin da na fi kauna ke nan, kuma ina samun nishadi da jin dadin kasancewata da yara.

Kana daya daga cikin shahararrun mawaka da duniyar Kannywood take ji da su, duk da samun wannan shaharar a ganin wadanne kalubale kake fuskanta?

Ka san kalubale da za a ce ana fuskanta kawai wani abu ne da za a ce ya bi jiki, abin da ya sa na ce ya bi jiki kuwa shi ne, duk mutumin da ya samu kansa a irin wannan mataki na shahara, da ma ya san dole zai samu farin ciki da akasin hakan, zai hadu da masoyi, zai hadu da wanda ba masoyinsa ba, iri-iren wadannan idan za ka rika hadawa, idan ka samu makiyi, to idan ka dubi masoyi sai ka kawar da kai kawai, tun da ba dole ne kowa ya soka ba, idan wani ya so ka, wani zai ga ba kai yake ra’ayi ba, to wannan ba wani abu ne da zai dame ni ba.

Ko izuwa yanzu wani shiri kake da shi na fitar da albam?

Tun da mun shiga sabuwar shekara, kamar yadda shirina yake wato duk farko sabuwar shekara nake sakin albam guda biyu haka, to a wannan ma zan sake albam guda biyu a watan Janairu. Sunan albam din ‘Wasika’ da kuma ‘Manyan Mata’.

Mene ne dalilin da ya sa ka sanya wa albam din sunan ‘Wasika’?

Gaskiya ni idan zan yi albam, nakan yi kokari in cusa sakon da zai zo daidai da sunan albam din, ba wai kawai sunan ne yake mini dadi ba, don haka sai in rubuta don ya ja hankalin mutane ba, mutane su zo su dauka su ji sabanin abin da suka ji, inshaAllahu duk da cewa ka ji an ce wasika, akwai yiwuwar wani sako za a tura a cika, ko ma dai wani iri ne, su masu sauraro za su ji a cikin albam din.

Yanzu kasancewar ka samu abokiyar zama, wane yanayi ne ka fi jin dadin gabatar da ayyukanka?

Da yake ni da ma ba ni da wani yanayi ko lokaci da zan ce na fi so in yi waka ko rubuta waka, kodayake da ma ni rubuta waka ma bai dame ni ba, kawai da ma idan na fita studio da zil din yin waka, to inshaAllahu zan yi, idan kuma ba ni da zil din yin waka, to ko da na tukara kaina sai na yi waka, to a karshe dai zan tashi in bar ta, to kusan kowane yanayi da nake so in yi waka, wato daidai lokacin da nake fita wurin aiki, in na fita  a wannan lokacin na san me zan yi, inda da na je zan fara, kuma cikin awannin da na dibar wa kaina inshaAllahu zan yi in gama, don haka samun abokiyar zama bai sa na na samu sauyi ta yadda na saba gudanar da ayyukana ba.

Kamar a yanzu kana da wani kuduri da kake so ka cimma?

To,  a gaskiya kuduri wanda a halin yanzu nake so in cimma ni a nawa ganin duk abin da nake so in cimma Allah Ya nufa ya cimma, sai dai kawai, ban san me Allah Zai yi gobe ba, amma ni a yanzu duk wani mataki da nake so in kai, to Allah Ya kai ni, tun da idan na dubi daukakar da Allah Ya yi mini da irin matsayin da nake da shi da masoya da Allah Ya ba ni da kuma yadda masoya suke karbar abin da nake yi, har in fitar da wani tsari na cewa sai shekara-shekara nake fitar da albam, babu wanda ya taba yin hakan a harkar wakar Hausa, kodayake ban sani ba imma an yi dai, to a yanzu ni ne na sa wa kaina wannan tsarin, kuma hakan bai sa masoyana sun guje ni ba, suna ma kosawa ne albam din ya fito, abin da na dauka shi ne waka ba abinci ba ne da za a ce kullum sai an ci, su bukatarsu in kawo musu, su ji dadi, ni kuma tsarina ne, ina son shi, kuma ina so in rika tafiyar da shi a haka. 

A karshe ko kana da wani kira da kake so ka yi ga masoyanka da kuma sauran jama’a?

Akwai abubuwa wadanda za ka ga sau da yawa ana dauko su a yaba mini, wani lokaci za ka ji an ce Nura ya mutu, wani lokaci ka ji an ce an sace ni, a baya kuma bayan na yi aure shi ma aka ce an dauke matata, to jan hankalin da zan yi ga mabiyana shi ne, sau da yawa akan kirkiro wadannan abubuwan don a rika daga musu hankali, ko kuma ni ma hankalina ya rika tashi, don in rika tsorata da wadansu abubuwa, hakan ya sa zai yi wuya a dauki lokaci mai tsawo ba a dauko wani abu da zai kawo razana a gare ni ko kuma ya tayar da hankalin masoyana ba, saboda haka su dinga hakuri da abin da suke ji, sannan idan sun ji to su dinga bibiya kafin su daga hankalinsu, wato su bi a saukake ba tare da sun tayar da hankalinsu ba, domin su tabbatar labarin da suka ji gaskiya ne ko karya ne, su kuma kiyayi watsa labaran karya.