✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa nake boye wasu abubuwa da suka shafe ni – Nafisa Abdullahi

Kwana biyu an ji ki shiru a finafinai, ko lafiya? To, gaskiya ba zan ce an ji shiru ba, kawai dai hutu ne kamar yadda…

Kwana biyu an ji ki shiru a finafinai, ko lafiya?

To, gaskiya ba zan ce an ji shiru ba, kawai dai hutu ne kamar yadda kowa yake yi. Kuma na yi hakan ne domin na mayar da hankali kan sabon fim dina da yanzu haka muke shiryawa, yana nan fitowa nan ba da jimawa ba. Fim ba don tsirarun mutane ake yi ba, ana yi ne saboda al’umma da yawa. Saboda haka, dole ana bukatar yin tunanin na kwarai ta yadda za a zo wa da mutane abin da za su yi saurin karba.

Finafinai nawa ne wadanda kike yi yanzu?

Ina da finafinai da yawa wadanda aka kawo min labarinsu. Ba komai ne zan bayyana ba dalla-dalla a halin da ake ciki yanzu. Albishirin da zan yi wa masu kallon shi ne, sabon shirin da muke kokarin zuwa da shi, hakika zai kayatar matuka da gaske.

Ko za ki iya shaida wa mutane sunan fim din?

To, yanzu dai mun rada masa suna KARMA.

Shin kun kusan kammala shi wannan shirin ne?

Zuwa yanzu zan iya cewa mun kammala kusan kashi 70 cikin 100. Amma ka san yanzu abubuwa sun canja, saboda haka muna da sabbin hanyoyi da muka bullo da su na tallata wannan fim da zai dace da yadda ake yi a fadin duniya. Mun ajiye tunanin kasuwancin fim da gama-gari. Wannan karo sabbin tsare-tsare ne da muke sa ran haska fim din a wasu kasashe, ba wai Najeriya kawai ba.

Yaushe za a saki fim din?

Ba zan fadi wannan ba a halin yanzu. Abin da na sani shi ne muna aiki tukuru don tabbatar da ganin mun kayatar da mutane. Lokaci ne kawai zai bada damar haka. Idan lokaci ya yi kowa zai ji labari.

Ko za ki dan yi tsokaci game da abin da fim din ya kunsa?

Ba yanzu ba tukun. Ina da dalilaina na boye wasu abubuwan da suka shafi lamari irin wannan kafin a kammala. A wasu lokutan, idan ka bayyana abu, a karon farko sai ka ga ka rage wa mutane karsashi. Amma ina tabbatar wa masu kallon cewa, Nafisa Abdullahi da aka saba gani, to a cikin wannan shiri ta canja, domin za ta bayyana ne a wata siffa daban. Shi ya sa nake ta fadi tunanin da muka yi ya ba mu damar kirkiro abubuwa da yawa. Duk lokacin da ka samu nutsuwar yin tunani, to babu shakka za a zo da abu mai kayatarwa.