✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa na sha gaban kowane furodusa a Kannywood – Sani Sule

Masana’antar fina-finai ta Kannywood ta hada mutane masu yawan gaske wadanda idan ka bincika za ka ga kowanne da irin tasa gudunmawar da yake bayarwa…

Masana’antar fina-finai ta Kannywood ta hada mutane masu yawan gaske wadanda idan ka bincika za ka ga kowanne da irin tasa gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban harkar, babu shakka haka masana’antar ta faro tun farkon kafuwarta har zuwa wannan lokaci, don haka duk inda ka duba a bangarorin sana’ar da take cikin harkar fim za ka tarar da wani jigo da ake ji da shi a wannan harkar.

Furodusa Sani Sule Katsina wani jigo ne da a yanzu za a iya cewar ya tattara bangarori da dama a harkar fim da a yanzu shi ne yake rike da su, ta yadda ya zama wani jigo da a masana’antar samun kamarsa zai yi wahalar gaske. 

Domin kuwa a yanzu duk da irin yanayin da harkar fim take ciki na durkushewa za a iya cewa shi ta harbi kasko, ssaboda a wannan lokacin ne yake sharafinsa, don haka ne ma kamfaninsa na Rite Time Multimedia ya zama wata kariya ga masana’antar Kannywood. 

A yanzu mafi yawa daga cikin kamfanin shirya fina-finai sun dade ba a jin motsinsu, wasu ma tuni sun canza sana’a, amma shi Sani Sule Katsina ya tsaya tsayin daka don ganin masana’antar ba ta kai ga faduwa kasa ba, don haka ne a yanzu ba dare ba rana kamfaninsa ya dukufa wajen samar da fina-finai masu inganci, wadanda suke karawa masana’antar kima a idon duniya. 

Ko me ma ya jawo shi zuwa wannan masana’anta da kuma irin burin da yake da shi? Sai ya ce, ita sana’ar fim sana’a ce mai kyau da za ka iya samun alheri a cikinta, kuma ka bayar da gudunmawa ga al’umma, ka fadakar da su hanya da ba su sani ba.

“Kuma ni a matsayina na furodusa, shirya fim kawai nake yi na zuba kudina na yi fim, akwai fina-finai da dama da na shirya irin su ‘Mafarki’ da ‘Ibro Ya Auri Baturiya’ da ‘Matar Mutum Kabarinsa’ da sauran su, amma da yake yanzu yanayi ya canza musamman yanayin faduwar kasuwar fim, sai na koma harkar gidajen Talabijin.”

Ya ce,  don yanzu zai iya cewa babu wani kamfani da yake shirya fina-finai mai dogon zango wato ‘series’, “kamar kamfanina mai suna Rite Time Multimedia, musamman idan kana kallon tashar Star Times, ka san shirin da ake nunawa mai suna ‘Kukan Kurciya’. To mu muka yi shi mun yi kashi na daya, ana nuna shi yanzu, sannan daga an gama za a ci gaba da nuna kashi na biyu, kuma ga wani babban fim shi ma da muka gama za a fara nuna shi nan gaba kadan mai suna ‘Sarauniya’, don wadannan ayyuka da muka yi karamin furodusa ba zai iya yin sa ba.”

Ya ci gaba da cewa, “Kasancewa ita harkar fim mai dogon zango sai da kudi mai yawa, muna son harkar kasuwar, amma dole muka bar ta, saboda tabarbarewar kasuwar da kuma masu satar fasaha, ka sanya kudi ka shirya fim ka gama ka kai shi kamfani a buga maka, kuma ka bada shi bashi a kasuwa, su ma su tura bashi, sai lokacin da aka ga dama za a ba ka kudinka ga kuma masu satar fasaha suna daka mana wawa, abin ma da suke yi mana ya fi karfin kashe mu raba, sai dai mu kira shi kura da shan bugu gardi da karbe kudi. 

Ya ce, can kuma kasuwa ba a sayar ba a mayar da maka da kayanka, don haka da suka ga duniyar ta canza wanda yana da wahala ka shiga gida goma ka samu hudu da suke kallon DbD sai dai tashoshin talabijin, don haka sai suka mayar da karfinsu zuwa shirya fina-finai masu dogon zango.

“Duk da cewa akwai bambanci mai yawa a tsakaninsu saboda shi fim mai dogon zango yana daukar dogon lokaci wanda za a iya shekara daya, shi kuma wancan don gutsure ne za a gutsura maka idan ma labarin ya gamsar da kai ko bai gamsar ba za a gutsure labarin ba, amma shi mai dogon zango sai ka shekara daya kana kallo, saboda cikakken labari ne ake daukowa, ya kai inda ake so ya kai, tun da mu Hausawanmu sun raja’a ga sayen fim mai dogon zango na Indiya, sai muka ga me zai hana mu yi na Hausa yadda za su karu da shi kuma ya maye na Indiya din da suke kallo.”

Ya bayyana cewa kuma a zuwa yanzu kwalliya ta biya kudin sabulu tun da zai iya cewa sun kama hanyar kai ga nasara don kuwa ba cika baki ba “ka je ka duba duk wani furodusa ka gani a yanzu za ka ga na sha gabansa, ka je ofishin sa ka gani za ka hada shi da nawa? Don haka na sha gaban duk wani furodusa a Kannywood, kuma ina gode wa Allah da wannan matsayi da Ya ba ni.”

Ya kara da cewa “Irin yadda jama’a suka gamsu ma da aikinmu shi ma shaida ne, don haka kungiyoyin matasa da dalibai da masu yi wa kasa hidima suke karrma ni da lambar yabo, musamman kungiyar Matasan Arewa da ta dalibai ’yan hidima.”

“Sannan ga shi a da taron da aka gudanar na bikin karrama ’yan fim na City People a birnin Legas ni ne na zamo furodusa na farko, sannan fim din ‘Kukan Kurciya’ ya zamo na daya a fim mai dogon zango da aka yi a wannan shekarar. Don haka muna rokon Allah Ya kara dafa mana a kan aniyarmu ta samar wa matasa aikin yi da kuma kyautata masana’antarmu ta Kannywood.” Inji shi.